Matsalar Tsaro Bata Hana Gwamnatin Jihar Yobe Aiki Ba –Lawan Shettima

LAWAN SHETTIMA ALI shi ne kwamishinan ayyuka a jihar Yobe, ya bayyana cewa matsalar tsaro bata hana gwamnatin jihar yiwa al’umma aiki ba, tare da batutuwa da dama, a cikin tattaunawar da yayi da wakilin mu MUHAMMAD MAITELA. Ga hirar kamar yadda take.

Yallabai, masu sauraro zasu so jin cikakken sunan ka tare ma’aikatar ka.

Kamar yadda aka sani, sunana Lawan Shettima Ali. Kwamishinan ma’aikatar ayyuka, sufuri da makamashi, a gwamnatin jihar Yobe.

 

Wadanne muhimman ayyuka ne wannan ma’aikata taka ta gudanar, na ci gaban al’ummar jihar Yobe?

Alhamdullah, duk mutumin da ya saka kafar sa a jihar Yobe zai tabbatar tare da nuna maka ayyukan da Maigirma gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam yayi- tun zuwan sa karagar mulki, tun bayan rasuwar marigayi Gwamna Mamman B Ali. Lakacin da ya zama gwamna tun cikin watan Janairun shekarar 2009. Ina tunawa ya fara da aikin tagwayen hanyar da ya zagaye Damaturu hadi da wutar lantarki mai amfani da hasken rana, wanda tsawon sa kilo mita 19 ne.

Sa’annan sai aka koma a manyan garuruwan jihar, misali a cikin birnin Damaturu da kanta inda aka shimfida tituna a rukunin gidajen ma’aikatan gwamnati ke zaune da sauran jama’a hadi da unguwannin da ya kamata ayi musu hanya a cikin babban birnin jihar. Sai kwaltar kawata birane wanda a Potiskum aka yi hanya mai tsawon kilo mita 14 hadi da magudanun ruwa kilo mita 24. Sannan sai a Nguru kilo mita 10 da magunanar ruwa kilo mita 20, Gashuwa ita ma haka, Gaidam 11 da magudanar ruwa 22, duk wadannan an yi su ne a karon farkon hawan sa.

Bugu da kari kuma, gwamnatin jihar Yobe ta bayar da hanyar Kariyari zuwa Bayamari ta zarce zuwa Gaidam, wanda da farko gwamnatin tarayya ce ta sa bakin kwalta da tsakuwa (ba a zuba dafaffiyar kwalta ba), shi ne sai muka dora mata kwalta mai tsawon kilo mita 109. Sai kuma gyaran hanyar da ta tashi daga Potiskum ta fada Jakusko zuwa Garin-alkali, kilo mita 150, wannan kwaltar ita ce hanyar da aka gina tun tsohuwar Borno a zamanin nulki Gwamna Muhammad Goni, kuma ita kadai ce hanyar da muka gada; tun bayan kirkiro Yobe. Wadannan sune manyan ayyukan da ya aiwatar a karon farko, bayan zaman sa gwamna.

Har wa yau kuma, sai kuma ayyukan tsakanin 2011 zuwa 2015, wanda aka gudanar da ayyuka masu dimbin yawa, musamman hanyar da ta keta tsakiyar sahara daga Kanamm zuwa Machina. An faro wannan hanya ne daga Kanamma zuwa Kafiya, kilo mita 55, wanda ya kai naira biliyan 8, sa’annan aka sake bayarwa daga Kafiya zuwa Yunusari- tsawon kilo mita 20 ne daga nan kuma aka sake bayarwa zuwa Yusufari wanda kilo mita 50 ne, to a haka za a rinka dorawa har a kai Machina- kuma yanzu haka an samu kilo mita 125. Insha Allahu muna sa ran dorawa daga inda muka tsaya zuwa Karasuwa, a cikin wannan shekara.

A hannu guda kuma, gwamnatin jihar Yobe ta shimfida hanyar da ta tashi daga Karasuwa zuwa Jami-maji, kilo mita 17 ne, sannan da wadda ta tashi daga Gashuwa zuwa Yusufari, mai tazarar kilo mita 31- hanya ce wadda gwamnatin tarayya ta fara tun kusan shekaru 10, inda daga bisani suka rubuto mana kan cewa ba za su iya yin ta ba, a lokacin Jonathan shi ne sai Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce bari a je ayi ta tunda jama’ar mu ne. Ga hanyar Gaidam zuwa Bukarti, wanda ya je ya hade da hanyar da ta ratsa sahara- kilo mita 31 ce. Sai hanyar Bayamari zuwa Yunusari mai tsawon kilo mita 45 da gwamnatin jiha ta shimfida ta.

Haka zalika kuma, an kammala gina hanyar Potiskum zuwa Damchuwa, kilo mita 18 da Maiduwa zuwa Gadaka mai tsawon kilo mita 12. Sai kuma shimfida titi da gada, daga Gadaka zuwa Guduwali kilo mita 40. Sannan da gina hanyar Buni-gari zuwa Bara (cibiyar karamar hukumar Gulani) wadda ita ma da fari gwamnatin tarayya ta bayar da hanyar amma akwai manyan gadoji biyu wanda ba a yi ba, musamman a garin Bula-Rafa, shi ne gwamnatin jihar Yobe ta dauki nauyin gina su, hadi da sauran kananan kwalbatocin da ba a yi ba, hadi da karashen kilo mita 8. Wadannan hanyoyin da makamantan su, duk maigirma Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ne yasa muka yi su.

 

Ka lisafto wasu daga cikin hanyoyin da kuka gina, mallakin gwamnatin tarayya, shin ko suna biyan ku?

To bari in karasa zancen hanyoyin gwamnatin tarayya ka ji, misali, kafin nan tukuna. Idan da ace da adalci ai ba Yobe ya dace ace mun gina hanyoyin da suka ratsa cikin sahara ba, saboda yadda ta kananan hukumomi biyar (5) zasu ci gajiyar su-Gaidam, Yunusari, Yusufari, Karasuwa da Machina. Sa’annan kuma kan iyaka da jamhuriyar Nijar ne muka yi wannan hanya; baya ga kuma yadda idan ba wanban hanyoyin jama’ar ba zasu iya fidda kayan amfanin gonakin su, dabbobi da walwalar su ta yau da kullum, wannan ne makasudin yin ta. Ka duba daga Nguru zuwa Machina kilo mita 50 ne tare da kwaltar cikin gari kilo mita 3 da magudanun ruwa. Ka ga duk wadannan guraren, daga wannan karamar hukuma zuwa waccan ai da gwamnatin tarayya ce ta kamanci tayi mana, amma a haka maigirma Gwamna ya yi hanyoyin.

Ga hanyar da ta tashi daga Damaturu zuwa Mazga (kan iyakar Yobe da Borno), kan hanyar Biu, kilo mita 77 mun kashe naira biliyan 6.5 aka gina ta, ita ma ta gwamnatin tarayya ce, duk da matsalar tsaro amma gwamnatin jihar Yobe ce ta gina ta. Yayin da ake cikin aikin kuma shi ne Boko Haram suka saka bam a gadar Katarko- suka rushe ta, dole aka kara wa dan kwangila naira miliyan 170, domin sake gina gadar. Na gwamnatin tarayya ne, kuma har yanzu ko sisin-kwabo ba a bamu ba, (ballantana sauran hanyoyin sahara, Nguru-Machina, Gashuwa-Yusufari da suka kasa yi) duk da a yan kwanakin nan sun ce zasu biya mu na gyaran gadar, tunda sun riga sun sashi a kasafin kudin su. Amma wata kila nan gaba su waiwaye mu da batun.

Kuma munyi wadannan ayyukan duk da karancin kudin da muke samu sannan uwa-uba matsalar tsaron da muka dade muna fama da ita, kuma duk wadannan basu hana maigirma Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam yiwa jama’ar sa aiki ba.

 

To me zaka ce a fannin makamashi, musamman yankunan karkara?

Ta hanyar hukumar REB, wannan ma’aikata tamu ta taka rawar gani ta fannin sada yankunan karkara da birane da hasken wutar lantarki. Kuma da yake yanzu mun canja salo, sabanin a da wanda bayan an ja wutar lantarki sai a saka injin bayar da wuta hadi da sayen mai kowanne lokaci, saboda yadda sha’anin mai ya baci. To ganin an samu karuwar wutar lantarki shi ne duk garin da ya kamata a kaima wuta ko a cikin wasu unguwanni da bayar da na’urar raba wutar idan ta samu matsala a wasu kananan hukumomi, muna kan yi.

Mun ja layukan wutar lantarki daga Damaturu zuwa Babban-gida zuwa Dapchi, kuma a wannan tsakanin akwai Lantewa da Kuromari da Kariyari duk an sauke musu wutar. Sa’annan daga Dapchin an ja turakun layin wutar zuwa Bayamari zuwa Balle da Kyalluri har Gaidam. Anyi wannan tunanin ne saboda yadda da farko layin wutar da ya isa Gaidam ya ratsa cikin daji ne, kuma idan an samu matsalar faduwar turakun wutar akan sha wahala. Shi ne ya jawo Gwamna ya amince da daukar matakin. A nan cikin babban birnin jiha, muna bi unguwa-unguwa an sauke wutar.

 

Duk da yadda wasu jihohi basu damu da habaka sha’anin sufuri ba, Ranka ya dade, yaya abin yake a jihar Yobe?

A nan Yobe muna da Yobe Line, duk da a gwamnatance muna kiran sa Yobe Transport Cooperation, duk da yadda har yanzu akwai yan gyare-gyaren da ya kamata a yiwa sashen, dangane da tafiyar da sha’anonin sa. To amma bai wuce shekaru 3 da suka gabata ba wanda gwamnatin jihar Yobe ta sayi motocin bus-bas sama da 20 domin saukaka lamurran zirga-zirgar jama’a da kayan su, wanda halin da ake ciki yanzu sun tsufa, kuma muna gyaran su. Har wala yau, muna sa ran cikin wannan shekarar gwamnatin jiha ta sake bayar da sabbi, domin ci gaba da bunkasa bangaren. Sannan mu sake zaunawa da kwamitin sufuri a majalisar dokokin jiha wajen yiwa dokar da ta samar dasu gyaran fuska.

 

Ina aka kwana dangane da shirin ku na gina babban filin jirgin sama na kasa da kasa?

Wannan aiki ne babba kuma wanda zai ci makudan kudade; domin a duka-guda ya dara sauran ayyukan, duk da kamar yadda na fada maka da farko, mun kashe sama da naira biliyan 100 wajen gina hanyoyi a jihar Yobe. A yanzu wannan babban filin jirgin sama (cargo) wanda gwamnatin jihar Yobe take ginawa yanzu haka- yamma da garin Kalalawa, mai tazarar kilo mita 25 daga Damaturu. An bayar da aikin watanni uku da suka wuce; bayan zaman majalisar zartaswa, kan tsabar kudi naira biliyan 11 da yan kai. Yanzu aikin yana gudana; gadañ-gadan, kuma bai wuce makonni biyu da Maigirma gwamna ya ziyarci warin da idon sa.

Sun kai kayan aiki tare da tifofi da motocin tonon kasa da makamantan su, sannan fara da aikin tagwayen hanyoyin da ya tashi daga babbar hanya zuwa cikin filin, wanda tsawon hanyar ya doshi kilo mita daya da mitoci 700. Kuma muna sa ran kammala aikin wannan filin jirgin cikin watanni 15.

Yayin da yanzu haka aikin ya kai kashi 20 da doriya daga cikin kaso 30 na fari da aka basu, kan kudi naira biliyan 3 da miliyan 100- an riga an basu kuma suna ci gaba da aikin kasa da kofar shiga filin jirgin da masaukin fasinja da sauran ofisoshi irin su na yan-sanda, yan kwana-kwana(ma’aikatan kashe gobara).

 

Ko zaka bayyana wa masu saurare karin wasu ayyuka da da wannan ma’aikata zata aiwatar a shekarar 2018?

Cikin yardar Allah, a cikin kasafin kudin da Gwamna Alhaji Ibrahim Gaidam ya saka wa hannu gwamnatin jihar Yobe ta kudiri aniyar kashe naira biliyan 17 da doriya wajen ci gaba da samar da muhimman ayyuka masu ma’ana ga al’umma. Bisa ga wannan kwangila ta gina filin jirgi ta biliyan 11 da yan kai- mun biya kaso 30 (N3.1bn) cikin dari na kudin ka ga yanzu abinda ya rage kusan biliyan 8 da wani abu ne yayi saura mu biya su. To wadannan kudin suna cikin wannan kasafi da aka yi. Saboda haka, a wannan shekarar zamu ci gaba kamar a da, kuma mu ko’ina aiki ne kaca-kaca.

Kuma wani abin alfahari mu a nan Yobe, shi ne Maigirma gwamna bai taba tunanin ciyo bashi a banki, tun ranar da ya zama gwama zuwa yau kuma nan gaba ma bashi da wannan tunani wajen cin bashin sisin-kwabon kowa. Sannan duk alkawarin da Alhaji Ibrahim Gaidam yayi wa jama’ar jihar Yobe ya cika shi, yayin da wasu ayyujan kuma ya yi su ne ba tare da alkawuri ba- ya umurce mu duk inda muka ga wani aikin da zai amfani al’ummar Yobe, mu sanar dashi kuma zai yi. Kuma duk ayyukan mu a zahirance suke, sannan bamu shakkkar nuna su ga kowaye- bamu da kwalo-kwalo, shugaban mu yana tafiya bisa kan gaskiya.

 

A karshe, na san ba zaka rasa abin fada ba, bisa kokarin jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya a wannan yanki ba?

Eh to, Alhamdullah, domin a matsayina na dan Yobe idan ban yaba da kokarin da suka yi ba, to ban yiwa kaina adalci ba. Domin sanin kowa ne kan cewa a cikin shekarun da suka wuce; musamman a 2011 zuwa 2014, wadannan shekaru ne da muka sha wahala, muka ga fitina da masifa da kowa ke gudu- ina zaune a nan sai muji aman karar bindigogi, ace gari ya baci, sai mu rinka tunanin daji zamu shiga ko zamu yi gida!

Yanzu gashi duk wadannan lokutan sun wuce; yau Alhamdullah, da kokarin su da yadda make addu’a Allah ya kawo muna zaman lafiya. Gaskiya dole zamu yabawa sojojin mu da yan-sandan mu tare da sauran jami’an tsaron kasar nan, muna addu’ar karin zaman lafiya, musamman a Yobe, mun ci moriyar addu’ar mu.

Baya ga tsayuwar maigirma gwamna wajen sawa ayi ta addu’o’i, sannan kuma gwamnatin jihar Yobe bata taba yin sakaci wajen goyon bayan jami’an tsaro ba, yayin da ko a cikin yan kwanakin nan saida ya basu motoci kirarar Hilud sabbi fil, sama da 20. Kuma a baya, a lokacin da gwamnatin PDP ta nuna halin ko oho damu, Maigîrma Gwamna bai fasa basu kudaden alawus din su da motocin aiki ba, duk lokacin da suka nema ya basu. Alhamdullah!

 

Exit mobile version