Muhammad Maitela" />

Matsalar Tsaro: Buhari Ya Sirrance Da Dattawan Borno Da Yobe

Minista

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya gudanar da ganawar sirri da kakkarfar tawagar dattawan jihohin Borno da Yobe a fadarsa, da yammacin ranar Talata.

Ana sa ran tattauna batutuwan tsaro ne za su mamaye ganawar, musamman yadda yankin ke ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro.
Bugu da kari, tawagar dattawan tana karkashin jagorancin Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da takwaransa Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ne. Haka nan, tawagar ta hada da tsohon gwamnan jihar Borno, Ashiek Zarma, Sanata Kashim Shettima, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai Elkanemi, Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa.
Sauran sun hada da karamin minista a ma’aikatar ayyukan gona, Mustapha Shehuri da karamin minista a ma’aikatar ayyuka da gidaje na tarayya, kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Yobe, Alhaji Abubakar Aliyu.
A hannu guda kuma, akwai sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari hadi da ministar ma’aikatar ayyukan jinkai da agajin gaggawa Hon. Sadiya Umar, duk suna cikin mahalarta taron.
A gefe kuma, Janar na yan-sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, babban mai bai wa shugaban kasa shawara (NSA) Manjor Janaral Babagana Monguno (mai ritaya) da Darakta Janar na DSS, Yusuf Bichi duk suna wajen taron.
Haka zalika, zaman ya kunshi tattauna batun yanayin tabarbarewar tsaron da ya addabi wadannan jihohin biyu tare da tattauna yanayin koma baya da yankin ya samu ta dalilin rikicin Boko Haram da yadda za a sake farfado da yankin.
Zaman taron ya yaba da nasarorin da sojojin Nijeriya ke ci gaba da samu a baya bayan nan a yaki da su ke da Boko Haram a arewa maso gabas.
Haka kuma ganawar ta tabo batun daukar matakai wajen sake tsugunar da yan gudun hijirar yankin zuwa garuruwa da kauyukan su, wadanda tsaro ya inganta, sake gina wuraren da matsalar tsaron ta shafa kana da sake gina wasu daga manyan hanyoyin mota mallakin gwamnatin tarayya a jihohin Borno da Yobe da sauran su.
Da yake zantawa da yan jarida, jim kadan da kammala ganawar, Gwamna Zulum ya bayyana cewa shugaban kasa ya basu tabbacin ci gaba da kai farmakin yaki da sojojin Nijeriya ke yi a maboyar yan ta’addan a jihar Borno da kowane bangaren yankin Arewa maso Gabas.

Exit mobile version