A ci gaba da kokarin da ake yi na gudanar da addu’o’i, domin neman saukin matsalar tsaro da kuma Annobar Korona da ta kara dawowa, Majalisar Mahaddata Alkur’ani Reshen Karamar Hukumar Wudil, karkashin Shugaban Majalisar Gwani Yakubu Hashim, sun shirya taron addu’o’i, kamar yadda Shugaban Majalisar Mahaddatan Alkur’anin na Kasa, Gwani Aliyu Saluhu Turaki ya bayar da umarni ga daukacin Alarammomin Kananan Hukumomin Jihar Kano 44.
Taron addu’ar da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata, a Babban Masallacin Juma’a na Garin Wudil, inda aka gayyaci Alarammomi 313 suka gudanar da saukar Alkur’ani 313 domin neman taimakon Allah da ya yaye mana matsalar tsaron da ke barazana ga ci gaban kasa baki-daya da kuma rokon Allah Ya dakile Annobar Korona, wadda a halin yanzu ta sake dawowa a karo na biyu.
Shi ma a nasa jawabin, Hakimin Wudil wanda Dagacin cikin garin Wudil Alhaji Mohd ya wakilta, ya jinjinawa kokarin Alarammomi bisa wannan gagarumar gudunmawa wadda ya ce ita ce kadai mafita ga matsanancin halin da al’umma ke fama da shi, saboda haka sai ya bukaci al’umma su kara himmatuwa domin gudanar da irin wadannan addu’o’i.
Alarammomi daga daukacin mazabu goma na Karamar Hukumar ta Wudil ne suka halarci taron addu’ar da kuma sauran wadanda aka gayyata duk sun halarci taron addu’ar.