Daga Rabiu Ali Indabawa,
Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, a ranar Asabar ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su guji duk wata ajanda da aka shirya don haifar da rarrabuwa da rashin zaman lafiya a kasar. Ministan ya yi kiran ne yayin da yake magana a wani shirin rediyo, wanda Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya sanya ido a Legas. Ya bukace su da kada su bari wani ko wata kungiya ta taka rawa a kan kalubalen tsaro a kasar da zai sa su fada da juna.
Mohammed ya ce kalubalen tsaro na kasar ya wuce kima, yana mai kira ga ‘yan kasar da su guji wasu kalaman da za su iya ta’azzara lamarin. “Muna kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su yi tir da duk wata manufa da za’a zo masu da ita don yin barazana ga hadin kai da zaman lafiya a kasar. “A ko da yaushe muna zaune tare cikin lumana har tsawon lokaci kamar yadda Hausawa, Yarabawa, Ibo, Fulani da sauransu, kuma a ko yaushe muna warware sabaninmu cikin ruwan sanyi.
“Don haka, Ina so in yi kira ga shugabanninmu na siyasa da na addini musamman da su yi taka tsan-tsan game da abin da suke fada. “Ya kamata mu kasance muna yin abubuwan da za su iya taimakawa wajen magance kalubalen tsaro da muke da shi, ba wai yin kalamai da ka iya dagula lamarin ba,” in ji shi.
Game da ‘yan bindiga da tayar da kayar baya kuwa, Mohammed ya ce gwamnati na iya bakin kokarinta don magance matsalolin. Ya ce hukumomin tsaro sun samu nasarori na ban mamaki a kan ‘yan fashi da ‘yan ta’adda, ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya su ba su goyon baya don yin hakan. “Idan muka kalli inda muke a da can da kuma inda muke a yanzu, za mu ga cewa an samu nasarori da yawa. “Duk da cewa har yanzu akwai kalubale, gwamnati ba za ta huta ba har sai matsalolin sun kare. “Ina so in yi kira ga ‘yan kasa da su ci gaba da ba da goyon baya ga gwamnati da jami’an tsaronmu don cimma nasarori,” in ji shi.