Daga Shehu Yahaya,
Biyo bayan matsalar garkuwa da dalibai da ’yan bindiga suka kaddamar a Jihar Kaduna, gwamnatin jihar ta bada umarnin rufe daukacin makarantun da suke karamar hukumar Kajuru har sai an samu saukin matsalar tsaro a yankin.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta fitar karkashin ofishin kula da ingancin ilimi na ma’aikatar, ta bayyana cewa, rufe makarantun ya zama wajibi bisa matsalar garkuwa da mutane da ake yi a yankin.
Sanarwa mai dauke da sa hannun Abigel Adze ta ce, “daga ranar 16 ga Maris, 2021, mun bayar da umarnin rufe daukacin makarantun da suke karamar hukumar Kajuru nan take, saboda matsalar masu garkuwa da mutane har sai yadda hali ya yi.”
A zantawarsa da Wakilin LEADERSHIP A YAU ta wayar tarho, Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Dakta Shehu Usman Makarfi, ya bayyana cewa, rufe makarantun a halin yanzu shine mafita ga dalibai bisa ganin yadda matsalar sace mutane take kara ta’azzara a wasu sassa na jihar Kaduna.
Kwamishinan ya ce, “Eh, da gaske ne mun bada umarnin rufe daukacin makarantun da suke karamar hukumar Kajuru, saboda kare rayukan dalibai bisa ganin yadda yankin yake fama da matsalar ‘yan bindiga.”
Dakta Makarfi ya kara da cewa, “ba makarantun gwamnatin kadai ba ne aka rufe, har da masu zaman kansu. Saboda haka muna umartar duk shugabannin makarantun da shugabannin malamai da su tabbatar da da cewa, sun bi dokar har sai lokacin da gwamnati ta bayar da sanarwa budewa.”
Ya ce, Gwamnatin Jihar Kaduna tana bakin kokarinta wajen tabbatar da matsalar tsaro ba ta haifarwa harkar ilimi matsala ba yana mai cewa, yanzu haka suna kokarin ganin an kawo karshen matsalar.
karamar Hukumar Kajuru an dade tana fama da matsalar rikice-rikice masu alaka da addini da kabilanci da kuma matsalar ’yan bindiga, wanda ya zama ruwan dare a yankin.
A ranar Litinin din da ta gabata sai da jami’an tsaron soja suka ceto wasu yara guda biyu da suka fada tarkon ‘yan bindiga a kananan hukumar Kajuru da Chikun.