Sace ‘yan makarantar kankara a jihar Katsina ya tuna min da makamantan sa da suka faru a shekarun baya, a wasu bangarorin da matsalar tabarbarewar tsaro ta shafa a kasar nan. Wadanda su ka ja hankulan yan Nijeriya da ma wasu kasashen duniya, tare da tsammanin daukar matakin dakile abkuwar makamancin su nan gaba, amma kuma sai hakan ya gagara.
dauki misali da harin sansanin sojojin Nijeriya da ke garin Metele, Baga, yan makarantar Chidok, yan makarantar Dapchi, harin kasuwar dabbobi ta Potiskum, harin Barikin Giwa, na Auno da na kwanan nan a garin Zabarmari da a makarantar kankara ta jihar Katsina, duk a haka su ke wakana kuma su wuce ba tare da daukar wani kwakkwaran matakin dakile sake aukuwar hakan ba.
1. Harin kasuwar dabbobi ta Potuskum
Cikin watan Mayun 2012 ne wasu maharan da ake kyautata zaton Boko Haram ne su ka kai wani mummunan farmaki a kasuwar dabbobi da ke garin Potiskum a jihar Yobe, wanda su ka yi amfani da bama-bamai da muggan makamai wajen kai harin, wanda ya jawo asarar rayukan sama da mutum 60 da raunaya kimanin 29 a farmakin da su ka kai da rana tsaka.
Bugu da kari, kasuwar shanu ta Potiskum ta na daya daga manyan kasuwanin dabbobi a Afrika ta yamma wadda yan kasuwa ke zuwa daga kowane yanki a nahiyar. A hannu guda kuma, wannan hari ne wanda ya daga hankalin yan Nijeriya matuka.
2. Kisan kiyashi a garin Baga:
Ranar 16 ga watan Afrilun 2013 garin Baga, da ke jihar Borno, ya fuskanci wani mummunan harin yan ta’addan da ya girgiza zukatan yan Nijeriya, wanda rahotanni su ka bayyana an kashe kimanin mutum 200 kana daruruwa su ka samu raunuka yayin da aka kona gidaje da cibiyoyin kasuwanci sama da 2000, wanda hakan ya jawo asarar biliyoyin naira a garin.
Kamar yadda bayanai su ka nuna, garin Baga babbar mahada ce kuma kan iyakar kasashen da ke makobtaka da Nijeriya kuma mashahuriyar mashigar da ta hada wasu kasashen waje da Nijeriya, baya ga kasancewar ta muhimmi a sha’anin kamun kifi, noma da sauran su.
3. Sace ‘yan makarantar Chibok:
Sace yan makarantar Chibok a jihar Borno, wanda ya faru tsakanin ranar 14 da 15 ga Afrilun 2014, ya na daya daga cikin manyan kalubalen da gwamnatin tsohon shugaban kasa Dr. Jonathan ta fuskanta kuma ya taimaka a zaben 2015 shi ne garkuwa da daliban makarantar su kimanin 276.
Wannan shi ne karon farko wanda matsalar tabarbarewar tsaron Nijeriya ta fito karara wanda kuma ya bude zazzafar muhawara a tsakanin yan Nijeriya da sauran kasashen waje. Al’amarin sace yan makarantar, ya sauya alkiblar da masana ke yi wa matsalar tabarbarewar tsaron Nijeriya, musamman yankin arewa maso gabas da ma kasar baki daya.
Duk da yadda sojoji su ka samu nasarar kubutar da wasu daga cikin daliban, wanda har yanzu da nake rubutun nan, wasu yan makarantar su na ci gaba da kasancewa ribatattu a hannun maharan; har yanzu akwai gurbin tabargazar sace yan matan a zukatan yan kasa. Har wala yau kuma, da yawan yan Nijeriya su na kallon zai yi wahala a samu makamancin hakan, amma kuma ina; har yanzu da sauran rina a kaba.
4. Harin ‘Giwa Barracks’:
Tun wajajen 2014 ne wannan babbar barikin sojojin Nijeriya da ke dab da birnin Maiduguri ke fuskantar kalubalen hare-haren yan kungiyar Boko Haram, wanda hakan ya kara tabbatar wa yan Nijeriya cewa: ‘Gobara Daga Kogi, maganinta Allah Sarki.
Wannan fa ita ce daya daga cikin manyan sansanonin sojojin Nijeriya a yankin arewa maso gabas da ke jihar Borno kuma wadda ta tara manyan zaratan jami’an tsaro, wadda ke zama garkuwa kuma babbar katangar karfen da ya dace kowa ya samu garkuwa daga cikin ta; amma kuma sai gobarar ta ratsa cikinta!
5. Harin masallacin Fage:
Ranar Jummu’ar 28 ga watan 11, 2014 wasu maharan Boko Haram su ka kai mummunan farmaki tare da tayar da bama-bamai a masallacin Fage, harin da mahukunta suka bayyana cewa ya yi sanadiyar rayukan sama da mutum 100.
Famraki ne wanda aka kai shi a wannan masallaci mai dadadden tarihi a babbar cibiyar kasuwanci a yankin arewa kana kuma daya daga cikin manyan birane a Afrika, ya girgiza kowane bangaren kasar tare da jefa fargaba da tsoro a zukatan jama’a, sannan hari ne wanda ya bayyana hakikanin tabarbarewar tsaron yankin arewacin Nijeriya wanda ya dace ayi wa tubkar hanci tun a wannan lokacin.
6. Harin Metele:
daya daga cikin mummunan farmakin da ya tsaya wa yan Nijeriya a kahon zuciya shi ne na Metele ta karamar hukumar Guzamala a jihar Borno- a wata ranar Litinin ta watan Nuwamban 2018 inda yan kungiyar Boko Haram su ka kai farmaki a sansanin sojojin da ke garin. Wanda duk da a hukumance ba a bayyana alkaluman sojojin da suka rasu ba, amma wata majiyar daya daga cikin sojojin da suka tsallaka rijiya da baya ya ce sun haura 50.
Ga wadanda su ka bibiyi rahotanni da bayanan yadda al’amarin ya faru, akwai matukar daga hankali tare da yadda sojojin mu ke fuskantar manyan kalubale a yakin da suke yi da matsalar tabarbarewar tsaro a yankin arewa maso gabas. Wanda wasu sojojin su ka nuna yadda suke fama da karancin kayan aiki da sauran abubuwan da suka shafi kula da su.
7. Garkuwa da ‘yan makarantar Dapchi:
A cikin watan Fabarairun 2018 ne yan Nijeriya su ka wayi gari da labari mafi daukar hankali, wanda ya bayyana cewa wasu mahara sun farmaki garin Dapchi tare da yin awon gaba da daliban makarantar sakandire ta kwana (GGSTC) sama da 100 da ke jihar Yobe.
A wannan shekarar, labarin sace yan matan shi ne kan gaba tare da kasancewa bako a tunanin yan Nijeriya wanda ya zo bayan faruwar makamancin shi a makarantar yan mata da ke Chidok a jihar Borno. Yan Nijeriya da sauran kasashen duniya sun bayyana alhinin yadda al’amarin ya faru tare da kiraye-kiraye ga gwamnati ta dauki matakin kubutar da daliban.
Wanda daga bisani yan kungiyar su ka dawo da yan makarantar garin da su ka dauke su, face daliba daya; Leah Sharibu wadda ta rage a hannun maharan.