Abubakar Abba" />

Matsalar Tsaro: Kungiyar Gwamnonin Arewa Ta Nemi A Kawo Karshen Rikicin Kudancin Kaduna

Filato

Gov. Simon Lalong

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya kuma wanda ya kasance shi ne Gwamna jihar Filato Simon Lalong ya  koka kan kai here-haer a Kudancin Kaduna.
Gwamna Simon Lalong ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da Darktan labaransa, Dakta Makut Macham ya fitar, inda  ya danganta hare-haren a matsayin abin bakin ciki.
Har ila yau, Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya Simon Lalong ya nuna damuwarsa kan yadda har yanzu ba a riga an kamo yan bindigan da suka kai harin a kauyukan Atyap guda hudu a karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.
A cewar Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya Simon Lalong, ya nuna damuwarsa kan yadda ake cigaba da kai hare haren duk da irin kokarin da gwamnatin jihar Kaduna da hukumomin tsaro suke yi na kawo karshen lamarin.
Simon Lalong ya yi nuni da cewa, hare- haren da aka kai wa kauyukan ya nuna cewa baya ga zaluntar mazauna kauyen da suke yi, bata garin sun dage domin ganin sun dakile kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi
don samar da zaman lafiya.
A cewar Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya Simon Lalong, Muna bakin cikin afkuwar hare haren da zubar da jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Ya ce, muna kira ga hukumomin tsaro su kare dage wa don kama bata garin, muna kira ga mazauna yankunan su taimakawa jamian tsaro da bayannan sirri da zai taimaka a kama bata garin. Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya Simon Lalong ya ce duk wata kungiya da ke ganin an mata ba daidai ba ta shigar da korafin ta
ta hanyar da ya dace a maimakon tayar da zaune tsaye da rikici. A cewar Shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Nijeriya Simon Lalong, a madadin kungiyar tamu, muna  isar da taaziyarsa ga  wadanda rikicin ya rutsa dasu da kuma ita kanta  gwamnatin jihar.
A karshe, Simon Lalong ya yi alkawarin taimakawa Gwamna Nasir El Rufai wurin aiki tare da wadanda abin ya shafa don kawo karshen rikicin, musamman a yankin na kudancin Kaduna.

 

Exit mobile version