Muhammad Maitela" />

Matsalar Tsaro: Majalisar Dattawa Na Neman A Sake Nazarin Yarjejeniyar ECOWAS 

Sanatoci

Majalisar dattawa tana neman Nijeriya ta sake nazarin yarjejeniyar shige da ficen da aka kulla tsakanin kasashen Afrika ta yamma wajen shawo kan kwararowar masu aikata laifuka cikin kasar nan, a ranar Laraba.

Majalisar, a bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai, mai dauke da sa hannun mai taimaka wa shugaban majalisar- Ezrel Tabiowo ta fannin aikin jarida a Abuja.

Sanata Lawan ya yi kiran a daidai lokacin da yake gargadi dangane da cusa kabilanci a matsalar garkuwa da jama’a hadi da ayyukan ta’addancin yan bindiga dadi a kasar nan. Wanda majalisar ta yi kiran ne a doguwar tattaunawar da ta gudanar a zauren kan kudurin rashin tsaro a fadin Najeriya.

Da yake gabatar da kudurin, Sanata Robert Ajayi Boroffice, daga jihar Ondo (APC), ya bayyana bakin cikin bisa rahotannin kashe jama’a da garkuwa da su a jihohin Ondo, Edo, Oyo, Imo, Kaduna, Zamfara, Niger, Nasarawa, Kebbi da sauran wasu jihohin kasar nan.

Bugu da kari, majalisar ta bukaci mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, sabbin shugabanin runduninin sojojin Nijeriya da Sufeto Janar na yan sanda, su gaggauta daukar matakan gano hanyoyin canza fasalin tsarin tsaron kasar nan da yadda ma’aikatan tsaro wadanda zasu taimaka wajen shawo kan matsalar musamman a kauyuka.

Haka zalika kuma, zauren majalisar ya yi kira ga gwamnonin jihohi da su mayar da kaimi wajen farfado da ingatattun ayyukan raya yankunan karkara tare da jawo al’umma kusa dasu wajen magance rikicin kabilanci, su kaddamar da sabon tsarin kiwo na zamani domin magance rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Har wala yau kuma, majalisar dattawan ta bukaci jami’an tsaro su yi amfani da jiragen sama maras matuki da jirage masu saukar ungulu wajen kula da dazuzzuka, wanda hakan zai taimaka wajen gano mafakar yan bindiga. Sannan kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakin gaggawa wajen dakile safarar makamai da tabbatar da dokar hana mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Ahmad Lawan ya gargadi yan siyasa da su guji siyasantar da matsalar tsaro zuwa ga kabilanci saboda kauce wa kawo rikicin da zai kai ga zubar da jini tsakanin kabilun kasar nan.

A karshe ya yi kiran a samar da karin kudade ga sojoji don su samu damar shawo kan matsalar rashin tsaro da ta mamaye dukkan sassan kasar nan.

Exit mobile version