Bello Hamza" />

Matsalar Tsaro: Masari Ya Bukaci A Dawo Da Majalisar Tsaro A Kauyuka

Islamiyya

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya bukaci a sake dawo da tsarin nan na majalisar tsaro a kauyuka tare da kara wa kananan hukumomi karfi don fuskantar matsalolin dake tattare da yaki da ta’addanci a yakin arewa maso gabas.
Masari ya yi wannan kiran ne a yayin da ya jagoranci ‘yan majalisarsa a ziyarar da suka kai sansanin sojojin nan na musamman dake garin Faskari wanda aka yi wa lakabi da ‘Special Army Super Camp 4’ tare a kuma ganin irin nasarorin da shirin nan na ‘Operation Sahel Sanity’ yake samu a yaki da ta’addanci a yankin.
Ya ce, gwamnatin jihar na duba yadda za a yi wa dokar kananan hukumomin na shekarar 1976 kwaskwarima ta yadda za a kara wa kananan hukumomi karfi a yaki da ‘yan ta’adda.
Ya ce, dole a karfafa kananan hukumomi don a samu tabbatar a zaman lafiya a fadin jihar.
Gwamnan ya kuma kara da cewa, har yanzu ba a kai ga fatattakar ‘yan ta’adda ba, ya kuma kamata a kara kaimi wajen ganin bayan ‘yan ta’addan.
A ranar Asabar ne kwamitocin majalisar wakilai da na majalisar dattawa suka kai ziyara sansan inda suka kuma as albarka tare da amince da kokarin da rundunar sojin take yi.
Bayan Gwamna Masari, ana sa ran Gwamnonin jihohin Kebbi, Kaduna, Sokoto, Neja da Zamfara da kuma sarakunan gargajiya za su ziyarci sansanin a cikin mako.

Exit mobile version