Akalla mutum 25,794 ne su ka rasa rayukansu a cikin shekaru hudu na mulkin shugaban kasa Buhari.
Kididdigar dai na dauke ne a cikin wata sanarwar bayani da wata kungiyar tantance harkar tsaro a Najeriya wato ‘Nigerian Security Tracker’, wacce ke karkashin kulawar majalisar kula da ayukkan kasa da kasa a kasar Amurka.
Adadin dai, na wadanda su ka mutu ne sanadiyar rikicin Boko Haram, kungiyoyon ta’addanci da kuma, wadanda su ka rasa ransu a sakamakon kisan wuce gona da iri na jami’an sojojin Nijeriya.
Daga watan Yunin 2015 zuwa Mayun 2019 a lokacin da Buhari ya karbi mulki kenan, an rasa rayuka a jihar Borno 9,303 kamar yanda wakilinmu ya nazarta, inda jihar Zamfara ke binta da 1,963 sannan jihar Adamawa da 1,529.
A cikin adadin a shekaru hudun, kungiyar Boko Haram ce tai sanadiyar 5,598, inda rikicin fulani makiyaya da sauran fadace-fadace yai sanadiyar 4,917.
A zamanin mulkin Jonathan daga shekarar 2011 zuwa 2015, an kiyasta akalla mutane 34,884 ne su ka mutu a fadin kasar, inda akalla mutum 12,765 su ka mutu imma dai sanadiyar Boko Haram ko kuma sojojin Najeriya.
A yayin da take bayyana madogarar kidayar ta ta, majalisar ta bayyana cewa, ta yi anfani ne da rahotannin kafafen sadarwa a matsayin madogarar tattara kidayar.
“Mun yi anfani da rahotannin kididdigar mako-mako na kafafen sadarwar Najeriya da na kasashen waje,” a cikin rahoton na majalisar.
Ta ci gaba da cewa, “kididdigar ta fara ne daga 29 ga watan Mayun 2011, ranar da aka rantsar da shugaban kasa. Muna daukar kididdigar ne mako-mako.
“Dogaro da rahotannin kafafen sadarwa wurin kididdage wa yana da nashi matsaloli, akwai banbancin samun tabbaci da hakikanin bayanai a tsakanin yankuna, a kan samu rashin takaimaimen adadin wadanda su ka mutu, sannan bayanin yanda abun ya faru ma ya kan babanta.”
Daga karshe, majalisar ta karkare da cewa, “Akwai kuma yiyuwar murda hakikar adadi ko dan saboda dalili na siyasa, kan haka, NST kan nemi bayanai daga majiyoyi daban-daban. Duk da haka dai, rahoto manuniya ce, ba wai hakikar adadin ba.”