Kamar yadda Nijeriya ke fuskantar kalubalen tsaro a halin yanzu, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, akwai bukatar dukkan hannaye su kasance a gefe guda don samun shugaban da zai iya samar da jagorancin da ake bukata don daidaita al’amuran kasar.
Ya yi maganar ne a ranar Alhamis, yayin da yake amsa tambayoyi daga masu magana da yawun Ofishin gwamnoni, bayan sun kaiwa gwamna Seyi Makinde ziyarar ban girma a ofishinsa.
Tsohon shugaban kasar, wanda ya kasance a Ofishin gwamnoni don kai ziyarar ta’aziya ga gwamnan kan rasuwar mahaifiyarsa, kuma ya je jihar ne don halartar wani taron kaddamar da littafi don girmama wani tsohon shugaban siyasa, Lamidi Adedibu, ya ce, mafi mahimmanci bangaren magance kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta shi ne shugabanci.
Ya kara da cewa, dubunnan kalubale a bangarorin tsaro, tattalin arziki da rikice-rikicen siyasa ba gaskiya ba ne kawai don sun dauki sabon salo. Obasanjo ya ce, “Akwai kalubale da dama a Nijeriya a yau. Akwai kalubalen tsaro, tattalin arziki, rikice-rikicen siyasa da sauransu. Wadannan kalubalen ba sababbi ba ne ayau, sai dai kawai sun dauki wani yanayi ne na daban.”
Lokacin da aka nemi jin ta bakinsa game da karin kiraye-kiraye na a kori shugabannin tsaro a matsayin wata hanya ta magance matsalolin rashin tsaro a kasar, tsohon Shugaban ya bayyana cewa, “Ban sanya shugabannin tsaro a ciki ba, ta yaya zan iya cewa a sauke su?”
Da aka nemi ya ba shugabannin tsaro da Shugaban kasa shawara, Obasanjo ya ce, “Idan ina da shawara ta uba ga shugabannin tsaro, ba zan ba su ta kafafen yada labarai ba.”
Yayin da yake magana a baya yayin ziyarar gaisuwar, Gwamna Seyi Makinde ya yaba wa Obasanjo kan kokarin da yake yi na ci gaban kasa, yana mai bayyana matakan da ya dauka na sauya fasali da inganta jihar, musamman a bangaren noma, tsaro, ilimi da kiwon lafiya, a matsayin abin koyi.
Makinde ya ce, “Muna son yi muku maraba da zuwa Ibadan. Mun yi kadan don bin sawun ka saboda manyan wuraren da gwamnatin jihar Oyo za ta fi mayar da hankali a kai sun hada da kiwon lafiya, ilimi, noma, kayayyakin more rayuwa da tsaro. Kuma noma a gare mu ita ce hanya daya tilo da za mu iya daukar jihar Oyo daga dogaro da kan so da tarayya ke bayarwa.”