Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Matsalar Tsaro: Obasanjo Ya Yi Zama Da Kungiyar Fulani

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ya shawarci ‘yan Nijeriya su daina nuna yatsa ga junan su sannan su hada kai wajen yaki da matsalar tsaro wadda ke barazana ga hadin kan kasar.
Obasanjo ya yi wannan batun ne ranar Asabar lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar Fulani mazauna kudu masa yammacin kasar a gidan sa dake Olusegun Obasanjo Presidential Library a garin Oke-Mosan dake Abeokuta.
Tsohon shugaban kasar ya ce hadin kan ‘ yan Nijeriya nauyi ne da ya rataya a kan kowa ba wai a iya kan gwamnati kadai ba.
Ya karar da cewa, dole a samu hadin kai a kasar kamar yadda yake a shekaru 1980 ta yadda za mu cigtaba da kasancewa abun koyi ga sauran kasashen Afrika.

Exit mobile version