Connect with us

LABARAI

Matsalar Tsaro: Rashin Kudi Ke Kawo Cikas A Yaki Da Boko Haram -Buhari

Published

on

Shugaba Muhammadu Buhari ya daura laifin rashin samun nasarar yakin yan ta’addan Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya kan rashin isasshen kudi a aljihun gwamnati.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin ganawarsa da kungiyar gwamnonin yankin Arewa maso gabas a fadarsa dake Aso Villa.

Ya kara da cewa cutar Korona ce ta kara tsananta lamarin.

Amma ya ce akwai damuwa matuka bisa yadda matsalar tsaro ke tsananta fiye da yadda ya samu abin lokacin da ya dau ragamar mulki.

“Muna da matsalan rashin kudi da rashin tsaro. Kun san gado mukayi. Amma ya kamata Al’ummar Arewa maso gabas su godewa abinda gwamnatin nan tayi.” Buhari yace

“Rahoton da nike samu, da kuma labaran leken asiri shine, hukumar Soji ta sake zage dantse kuma wannan shine gaskiyan lamari.”

“Ina tabbatar muku da cewa gwamnati na iyakan kokarinta. Rashin kudi ya zame mana kalubale.”

A bangare guda, Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya bayyana cewa jami’ansa sun fitittiki yan ta’addan Boko Haram daga dukkan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya face jihar Borno.

Hafsan Sojan, ya kara da cewa yanzu haka jami’ansa na amfani da labaran leken asiri domin kawar da yan ta’addan daga Borno.

“Babu yan Boko Haram a sauran jihohin dake makwabtaka. An fitittikesu, yanzu suna boye a jihar Borno,”

“Muna aiki tare da masu fararen hula da sarakunan gargajiya, abinda muke bukata kawai shine hakuri. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba.”
Advertisement

labarai