Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Duniya Tana Kallonka…! (2)

Asibitoci

Tare da El-Zaharadeen Umar,

Halin da talakawa su ka shiga a makon da ya gabata a sassa daban-daban na kasar nan, ya kara nuna cigaba da kasawar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar kasar nan baki daya.

Munin kashe-kashen makon da ya gabata ne ya kai ga Wole Soyinka fitowa ya bayyana cewa Najeriya fa ta rufta yanayin yakin Basasa, amma gwamnati ta kauda kai ba ta yarda yaki ne ake yi gaba-gadi ba.

Duk acikin makon da ya gabata kididdigar labarai ta bayyana cewa an kashe akasarin talakawa 239 kuma aka yi garkuwa da mutum 44 duk a cikin mako daya kuma da yawan wadannan ta’adanci sun faru a yankin arewa inda shugaban kasa ya fito.

Idan muka duba a jihar Zamfara kawai an kashe mutanen karkara sama da 90 a hare-hare daban-daban a magami da kewaye, cikin karamar hukumar Gusau, a Jihar Yobe kuwa Boko Haram sun yi dirar mikiya a Geidam, garin haihuwar sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali sun yi wa muatnen garin kisan mummuke tare da korar da yawa.

Ita ma jihar Oyo da ke kudu maso yammancin Najeriya ‘yan bindiga ne su ka tare hanya su ka yi garkuwa da dukkan fasinjoji 18 da ke cikin wata motar haya domin neman kudin fansa, kasa kamar ba gwamnati.

Matsalar tsaro ta kai ga an kai hari da rokoki a gidan gwamnan Imo Hope Uzodinma, kamar yadda a baya aka taba kai wa jerin gwanon motocin Samuel Ortom na Benuwai hari a cikin daji.

Irin haka ta faru da Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum, ba sau daya ba an kai masa hari kuma na yi asarar rayuwa da dama, har wani kwamitin bincike aka kafa domin bayyana gaskiyar abinda ya faru amma shiru kake ji kamar an aiki Bawa garinsu.

Allah jihar Katsina ma mahara sun yi garkuwa da mata su 20 da su ka halarci bikin radin suna, abinda rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta fito fili ta ce wannan al’amari wai bai faru ba, maimakon a dauki matakin ganin cewa an kwato wadannan mata sai ma aka rika tada jijiyoyin wuya akan ‘yan jaridun da suka bada labarin

Haka ita jihar Kaduna da gwamnansu ya ce babu shi ba sulhu da ‘yan ta’ada saboda haka duk wanda tsautsayi ya fadawa aka sace shi sai dai a bishi da addu’a sabanin wasu gwamnonin da suka nuna tausayin da jin kai suka biyi kudin fansa domin ceton rai, duk da haka ‘yan bindiga sun saci daliban jami’ar Greenfield kuma su ka kashe wasu daga cikin su.

Matsalar tsaron da ke ci gaba da faruwa ta nuna canja manyan hafsoshin tsaro da kuma canja Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, duk an ki cin biri ne, an ci dila, domin kamar yanzu ne aka fara wannan aika-aikata da ‘yan bindiga da mahara ke yi a Najeriya musamman arewancin Najeriyar.

Saboda haka ‘yan kasa sun fara tunanin cewa yanzu dai sun fara gano wadanda suke mulkin wannan kasa ba wai wanda suka zaba ba kuma suka sani ba, saboda haka akwai takaici matuka da har irin wannan magana tana fitowa daga bakin wanda yasan wannan matsala tun kafin hawansa mulki

Bayan haka wadanda aka dorawa alhakin tafiyar da sha’anin tsaro bayan wai ace sun kasa ba, har ta kai ga cewa wadannan mutane ba abinda yarda bane, ba irin mutanen da ya kamata ace an baiwa amanar ‘yan Najeriya ba ne, kusan mutun miliyan 200 a hannunsu haba jama’a!.

Kullin ana jin irin makudan kudadan da ake dankara masu da sunan samar da tsaro a kasa musamman yankin arewa, amma labarin dai daya ne, an kashe mutane kaza, an sace mutane kaza, an yi fashi da makami a gari kaza.

Shin wai don Allah ina wadannan kudade suke makalewa, me ake yi da su,? Babu wannan amsar sai dai ka ji an ce ‘yan jarida na kara ruruta wutar abu, bayan kuma wai bai kai haka ba.

Sai dai su ma din masu wannan zargin, har yanzu babu karin haske game da irin kudadan da ake mika masu domin baiwa jami’an tsaron da ake turawa wajan wanzar da zaman lafiya a wuraran da ake fama da wannan matsala.

Tuni dai ‘yan Najeriya na kallon matsalar tsaro a matsayin wata annoba da Allah ya kawowa har sun fara sake tunani game da haka, yanzu ana iya cewa kallon ya koma sama, saboda akwai lauje cikin nadi game da wannan bakar harka.

Yanzu kowa na ganin wannan harka ta tsaro ta koma wani sabon kasuwancin a tsakanin manyan jami’an tsaron Najeriya da wasu kuma wadanda suke boye a bayansu suna shan jini al’umma da suna ba su kariya a nan duniya.

Duk lokacin da ‘yan kasa suka koka game da abubuwan da ke faruwa ba zaka taba jin wadannan mutane sun goyi bayan su ba, ba zaka taba jin sun yi magana a dauki wani mataki ba, ba zaka taba jin sun yi wa al’umma jaje ba, suna kallon ana kashe jama’a amma ko a kwalar rigarsu.

Ya Allah muna rokonka albarkacin wannan wata mai albarka ka ji tausayin bayainka game da wannan babar matsalar da ta zama gagarau ga mahukunta Najeriya Allah Ya shiga tsakanin na gari da mugu domin samun rayuwa mai aminci a tsakanin bayainka Allah.

Exit mobile version