Connect with us

LABARAI

Matsalar Tsaro: Shugaba Buhari Ya Yi Alkawarin Murkushe ‘Yan Ta’adda

Published

on

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin samar wa rundunar sojin kasar nan da sauran rundunonin tsaron Nijeriya kayan aiki don su samu nasarar murkushe ayyukan ‘yan ta’adda a fadin tarayya kasar nan.
Bayanin haka ya fito ne a sanarwar da jami’in watsa labaran shugaban kasa, Garba Shehu, ya raba wa manema labarai jiya Juma’a.
Shugaban Buhari ya ce, lamarin matsalar tsaro a wasu sassa na tarayyar kasarnan yana matukar tayar da hankaIi musamman a bangaren Arewa Maso Yammaci da kuma Arewa Maso Tsarkityar kasar nan.
Ya bayar da wannan tabbacin ne jin kadan bayan kammala Sallar Idi tare da iyalansa a fadar Gwamnatin tarayya dake Abuja ranar Juma’a, ya kuma ce, lallai an samu gaggarumin nasara a kokarin samar da tsaro a kasar nan musamman ganin abin da aka gada a shekarar 2015 na matsalolin tsaro a kasar nan baki daya, amma tabbas akwai bukatar a kara kaimi don cimma abin da ake bukata.
Ya ce, ganin irin matsalar tsaron da muka cimma a lokacin da muka karbi ragamar mulki tabbas al’ummar da ke a yankin Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya za su jinjina wa kokarinmu amma lallai akwai abubuwan da ya kamata mu kara gabatarwa don lamarin a halin yanzu yana da tayar da hankali.
Ya kuma ce, shugabanin rundunojin tsaro na iyakar kokarinsu.
“Muna kokarin samar musu da kayan aiki don su kara kaimi a ayyyansu muna kuma kara zaburar dasu don su kara kokari a kan abin da suke yi.”
A kan cin hanci da rashawa, Shugaba Buhari ya ce, za a tabbatar da bincikar dukkan badakalar cin hanci da aka aikata a baya yadda ya kamata.
“Akan haka muka kafa kwamitin bincike, an samu cin amana daga ma’aikatar da gwamnatin baya ta amince dasu da kuma wadanda muka amince da su,” inji shi, ya kuma tabbatar da cewa, za a binciki tare da hukunta dukkan wadanda aka samu da cin amanar dukiyar al’umma.
Advertisement

labarai