Connect with us

NAZARI

Matsalar Tsaron Arewa: A Na Iya Samun karancin Abinci Bana

Published

on

“Na Duke Tsohon Ciniki, Kowa Ya Zo Duniya Kai Ya Tarar!” Babu shakka noma tushen arziki, na fuskantar barazana tare da Jefa al’ummar Najeriya cikin tsoro da fargaba. Haka na faruwa ne, sakamakon yadda manoma suka sami kansu hare-hare daga ‘yan bindigabindiga, yayin da haka ya jefa manoman cikin tsoro da Firgici.

Duk kokarin da Gwamnatin Tarayya take na kokarin ganin Harkokin noma ya inganta a Najeriya, amma kokarin nema ya ke ya zama “baya babu zane, saboda barazanar  rashin tabbas na tsaro. Duk manoman da ka shiyyar Arewacin Najeriya ya na kwana cikin rashin tabbas, musamman lokacin da ya ke kan Hanyarsa ko kuma yana gona domin gudanar da aikina na noma Shiyyar Arewacin Najeriya.
Idan Gwamnati bata tashi tsaye ba wajen shawo kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Kogi da Naija, da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Yobe da Borno da Gombe da Adamawa da Taraba da Taraba da Benue da Plateau da kuma jihar Nasarawa, wadannan jihohi na Fuskantar matsalolin tsaro, yayin da haka na zama barazana ga manoman
shiyyar.
Akwai bukatar gwamnati ta yi duk abin da za ta iya wajen ganin Manoman Shiyyar Arewacin Najeriya, sun sami cikakken tsaro domin samun damar gudanar da aikin noma cikin kwanciyar hankali. A wadannan jihohi da ke Shiyyar Arewacin Najeriya na fuskantar barazana tare da rashin kyakkyawan tsaro wanda ya ya ke zama barazana ga manoman yanki.
Hakika idan manoman shiyyar Arewacin Najeriya ba su sami damar aikin gona ba akwai alamun samun karancin amfanin gona a daminar bana.
Mu dubi yadda wadannan jihohi suke samar da kashi 60 daga cikin dari na abincin da ake noma wa a Najeriya rashin samun damar gudanar da noma a yankin zai kawo koma baya a Najeriya Gwamnatocin da ke wadannan jihohi idan basu tashi tsaye ba, wajen tabbatar da harkokin tsaro sun inganta a wadannan jihohi, babu shakka al’umomin da ke Shiyyar za su fuskanci karancin abinci a kakar bana. Ko da ya ke Jami’an tsaro
da suke aikin tabbatar da tsaro akwai bukatar kara zage dantse tare da nuna babu sani babu sabo yayin gudanar da aikinsu.
Haka kuma dole Sarakunan gargajiya su tashi tsaye tare da sa ido akan fadan Fulani da makiyaya domin samun amfanin gona. Yawaitar fadan fulani da Makiyaya yana juyewa ya zama na kabilanci, haka yana jawo koma baya a noma.
Shiyyar Arewacin Najeriya ya zama wani dandali na ta’addanci ganin yadda a ke kashe bayin Allah ba su ji ba, ba su gani ba. Sakamakon ta’addancin ‘yan bindiga a jihohin Kebbi da SOKOTO da Zamfara da Katsina a halin yanzu Manoman sun shiga fargaba tare da tsaron harin ‘yan bindiga a jihohinsu.
Haka zai janwo babbar asarar amfanin gona a yanki, tare da tashin tsadar Kayan abinci a tsakanin al’ummar Jihohin. Akwai bukatar gwamnatin Tarayya karkashin jagoranci shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tashi tsaye kuma ta dauki matakan ko-ta-kwana wajen ganin sun tanadi wadatacen abinci domin sayarwa da talaka  cikin Sauki, domin ko shakka babu harkokin noma a jihohin Kebbi da Sokoto  da Zamfara da Katsina da Yobe da Borno da Gombe da Adamawa da Taraba da Plateau da Nasarawa da jihar Benue  sun shiga cikin wani hali na rashin tabbas ta fuskar noma.
Duk da cewa gwamnati ta aika da jami’an tsaro wasu jihohin kamar Zamfara da Katsina da Kaduna da sokoto, idan ba a yi hankali ba, Manoman yanki za su zama cikin tsoro da fargaba ganin yadda jam’an tsaro ke kaiwa da komowa a wadannan jihohi.
Manoma da ‘yan kasuwa a arewacin Najeriya sun fara kokawa ganin yadda za su fuskanci matsala a wannan damina saboda matsalar rashin tsaro. Kokarin da Gwamnati ke yi wajen tabbatar da tsaro a shiyyar arewa akwai bukatar wayar da kan manoma su fahinci cewar jami’an tsaro da aka jibge a jihohin su, an yi haka ne domin kare lafiyarsu da dukiyoyinsu domin su kwantar da hankali tare da mayar da hankalinsu aka harkokin noma.
Shirin da Gwamnatin Buhari ta bulo da shi na hana tare  da daina shigowa da kayan abinci kasar nan zai gamu da cikas idan har ba a tabbatar da tsaro a shiyyar Arewa ba, domin basu damar gudanar da harkokin noma gadangadan a yankin.
Wannan ba shine karo na farko da mahukuntan kasar a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari za su dauki irin wanan mataki na tabbatar da tsaro ba, ya zama tilas gwamnati ta kara kaimi saboda wadannan ‘yan bindiga kan fake da duhun amfanin gona wajen cin zarafin manoma tare da gudanar da yakin sari ka noke.
Manoma a Jihohin Arewa  sai dai su bar baya babu zani, domin masu kama mutane su yi garkuwa da su sun hana su yin noma, akwai bukatar shugaba Buhari da ya tashi tsaye ya yi maza maza ya magance harkar tsaro domin a ci moriyar wanan lokaci na damina, in ba haka ba zai yi wuya a ci nasara.
Lallai ne manoma su bi shawarar jami’an tsaro yayin da suke gudaanar da harkokin noma, musamman wajen sauraro tare da tona asirin bata gari a cikinsu.
Wani Kwararre a fanin tattalinarziki Yusha’u Aliyu ya ce duk kasar da ta keso ta ciyar da kanta kuma a samu zaman lafiya dole ne ta dauki irin wannan mataki domin ta samu kudaden shiga daga kasashen waje saboda farfado da tattalin arzikin ta.
Saboda manoman da suka fito daga shiyyar Arewacin Najeriya kamar jihar Kebbi da SOKOTO da Zamfara da Katsina da Yobe da Borno da Gombe da Adamawa da Taraba da Plateau da Nasarawa da jihar Benue sun bukatar tallafi tare da kulawa ta musamman wajen samar da tallafi ganin yadda suke fama da ‘yan bindiga a shiyyar.
Advertisement

labarai