Connect with us

LABARAI

Matsalar Tsaron Katsina: Kwamishin ’Yan Sanda Ya Tarbi Masu Zanga-zanga

Published

on

zanga-zangar katsina

Tun da sanyin safiya jiyar Talata gamayyar kungiyoyin matasan Arewa su ka shirya wata zanga-zangar lumana, domin nuna damuwa a kan yadda ’yan bindiga su ke kashe jama’a a Jihar Katsina ba tare da daukar mataki ba, kamar yadda su ka bayyana.

Wannan zanga-zanga ta gamu da cikas a daidai lokacin da za a fara ta, inda a ka ga jami’an tsaro sun killace duk wata hanya da za ta kai mutun filin Kangiwa, wajen da a ka bayyana a sanarwa cewa daga nan ne za a fara wannan zanga-zanga ta lumana. Sai dai kuma hakan bai hana yiwuwar jerin-gwanon ba.

Masu zanga-zangar dai su na tafiya su na rera wakoki a kan manyan titinan Katsina su na cewa, su tsaro su ke so a Jihar Katsina da ma arewancin Najeriya, saboda yadda lamarin kullum sai kara lalacewa ya ke ta hanyar kai sabbin hare-haren wuce gona da iri da ‘yan bindiga ke kaiwa .

Wannan zanga-zanga irinta ce ta farko da gamayyar kungiyoyin matasan Arewa su ka shirya, domin nuna fushinsu a kan rikon sakainar kashi da su ke ganin gwamnatin ke yi wa harkar tsaro, musamman Gwamnatin Tarayya, wacce alhakin samar da tsaron kasar ya fi rataya a wuyanta.

Duk da irin barazanar da wannan zanga-zanga ta fuskanta, ta yi nasarar isa bakin kofar shiga gidan Gwamnatin Jihar Katsina, domin isar da sakonsu, bayan sun tsallake abinda su ka kira neman fada da wasu matasa da su ka tsokane su a kan hanya.

Malam Jamilu Charanchi na daya daga cikin shuwagabannin da su ka yi magana a gaban gidan gwamnatin, inda kwamishinan ’yan sanda na Jihar Katsina, Sunusi Buba, ya tarbe su a madadin Gwamna Aminu Bello Masari.

Ya ce, babban abinda ya sa su ke shirya wannan zanga-zanga shi ne, domin su sanar da Gwamnatin Jihar Katsina da kuma ta Tarayya cewa, rayukan jama’a a jihar sun koma kamar rayukan kiyashi; a kowacce rana, a kowocce awa, a kowane lokaci sai an kashe mutane, kai ka dauka cewa babu gwamnati.

Jamilu Charanchi ya cigaba da cewa, rayukan al’ummar Jihar Katsina sun zama abin wasa, inda ya ce, ba su yarda ba, ba su aminta ba – ba su gamsu ba cewa gwamnati ta daukin rayukan jama’ar Jihar Katsina da muhimmanci.

“Abinda mu ke ganin a kasa kai ka ce wannna gwamnati akwai ’ya‘yan Mowa da Bora, wanda mu mu ka dauka cewa gwamnatin jiha da ta tarayya ba ta yi ma na abinda ya kamata ba. Saboda haka mu na kira ga Gwamna Masarai da Shugaba Buhari su sani cewa, mulki zai kare, za su yi bayanin duk abinda ya faru a gaban Allah,” in ji shi.

Shin kowane irin sako ne su ke da shi tare da shawara a kan yadda za a shawo kan wannan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa a bangaren tsaro, musamman wannan yankin Arewa maso Yamma? Sai ya kara da cewa, su na da shawara da su ke son ba gwamnati da ta shafi harkar tsaro, inda ya ce, su na son gwamnatin ta duba batun kwamitin tsaro ta waiwayi baya ta duba duk abinda a ka gudanar a kan wannan matsala.

Ya ce, yakamata a binciki kwamitocin tsaro na Jihar Katsina, idan mutanen da ke cikin sun gaza a canza wasu, idan kuma su na yin aikinsu, shikenan a bar su, su cigaba.

Malam Jamilu Charanchi ya ce, ba su shirya wannan zanga-zanga ba, domin wani ko wata jam’iyyar siyasa ko domin jin haushin wani ko wasu, sun shirya ne saboda manufa guda; ita ce ‘yan Adam, saboda haka su na fatan cewa a gyara wannan bangare na tsaro.

Sai dai a nashi jawabin a madadin gwamna jJihar Katsina, Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Sunusi Buba, ya bayyana cewa, babu wanda ya kai shuwagabannin damuwa da wannan matsala ta tsaro da ta addabi Jihar Katsina.

Haka kuma kwamishinan ya ja kunnen masu wannan zanga-zanga da cewa, kada su bari a yi amfani da wasunsu wajen tayar da zaune tsaye, inda ya ce, duk wanda su ka kama ya na kokarin tayar da fitina, to fa ya kuka da kanshi.

An dai yi zanga-zangar ta lumana cikin lafiya ba tare da wata hatsaniya ba. Yanzu dai abin jira a gani shi ne, irin sabbin matakan da gwamnatoci a matakin tarayya da jihohi za su dauka, domin murkushe ’yan ta’adda da ke neman gagara.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: