Bello Hamza" />

Matsalar Wutar Lantarki Na Hana Karuwai Ciniki A Delta

Mazauna wasu yankuna a garin Warri da Effurun dake jihar Delta sun kasance basu da wutar lantarki na tsawon kwanaki a kan haka ne suka ba hukumar samar da wuta na yankin BEDC wa’adin kwanaki goma na a warware musu matsalar ko kuma su shiga zanga zanga babu kakkautawa.
Bangaren da rashin wutar ya shafa sun hada da Kosimi can kusa da filin jirgin sama da kuma Enerhen a unguwar Ubwie da kuma wasu wurare masu yawa kamar dai yadda wani mazaunin yankin, Cif Akpojotor Adjarho ya bayyana, ya kuma ce, matsalar rashin wutar ya matukar shafar rayuwarsu musamman yadda suka yi rayuwa a wannan lokacin da ake harkar zabe, ya kuma nuna takaicinsa a kan tunanin su na cewe, lamarin na iya ci gaba da karamari in har ba a dauki gaggarumin mataki ba a kai.
Haka kuma wani mazaunin yankin mai suna, Dabid Oke ya yi korafin cewa, cuwa-cuwar da wasu ma’aikatan hukumar BEDC ke yi, ya taimaka wajen haifar a matsalar a ake fuskanta, a kan haka ne ya shawarci hukumar ta gaggauta inganta harkokinta don kaucewa, fuskantar zanga zangar da aka shirya.
Amma jami’ar watsa labarai na hukumar BEDC, Misis Esther Okolie, ta mayar da martani, inda ta tabbatar wa da abokan huldar su kara inganta harkokinsu da kuma warware dukkan matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu.
A wata sabuwa kuma, kungiyar mara masu zaman kansu, ‘Commercial Sed workers’ dake yankin Abraka sun koka a kan yadda ake samun karancin masu neman amfani da su, suna kuma cewa, harkokin sana’ar ta su ya yi matukar faduwa a ‘yan tsakanin mako biyu da suka gabata.
Matan masu zaman kansu wadanda suka tattauna da manema labarai sun bayyyana cewa, wannan matsalar ta sa yawancin su suka canza sheka zuwa wasu bangarorin jihar don ci gaba da sana’ar su ba tare da wani matsala ba.
Bayani ya nuna cewa, ‘rundunar yan sanda sun fara cikakken bincike a yankin Abraka in da ake zargin samari yan damrfara da aka fi sani da Yahoo Yahoo boys su ke amfani da matan da kuma yin tsafi da su, hakan ya sanya mata karuwai suna gudu daga yankin don kaucewa fadawa.
Wata daga cikin karuwan mai suna, Chinoye Egbo, da ta bayyana albarkacin bakinta, ta ce, harkokinsu ya yi matukar faduwa ya kuma yanje baya tun da aka fara farautar ‘yan Yahoo Yahoo boys, don kuwa ‘yan Yahoo Yahoo boys sun fi biyan kudade, muna kuma tunanin sake unguwa da za mu ci gaba da harkar mu na karuwanci in da za mu samu kasuwa sosai,”

Exit mobile version