Connect with us

Madubin Rayuwa

Matsalar Yawan Cin Bashi Ga Mata A Zamanin Nan

Published

on

Yau filin zai yi tsokaci ne akan bashi (rance). Da yawa mata a wannan zamani kan fada harkar cin bashi na ba gaira ba dalili. Daga baya su yi ta haduwa da matsalolin rayuwa.

Wata mace ba ta rasa komai ba a rayuwar ta, mijinta na iyakar bakin kokarinsa don ganin ta samu rufin asiri da kwanciyar hankali, amma a haka sai ta fita ta nemi bashi saboda abin ya bi jikinta. Mata da yawa kan samu kansu cikin halin kunci ta dalilin bashi, wasu kan tsallake ma su bar gidajen su da ma garin bakidaya. Mafi aksarin masu wannan hali ta cin bashi ba sun nemi wani abu sun rasa bane sai don kawai haka suka daukarwa rayuwarsu. Wasu kan fada karbar kudi kama daga banki har zuwa gidaje wurin masu sana’a, daga baya a do ana samun matsala wurin biya. Ko kuma wata ta ga  kawata tayi wani abu wanda ita  ba ta  da hanyar sa ko mijinta ba shi da hanyar yi ma ta, ta ce dole sai tayi wannan abin ta hanyar cin bashi.

Mata masu wannan dabi’a ta yawan cin bashi da har yake hana mana zama cikin gidajen aurenmu muna sayawa kanmu rashin mutunci ne, da gori wa yaran da muka haifa. Ba komai ake nema a rayuwa a sameshi ba mu san wannan, sannan ba duka abinda muka kwallafa rai a kai ne yake zama alheri a garemu ba. Domin mata da yawa na zaman gidan kaso dalilin rashin iya biyan bashi, walau na kudi ko na kaya. Babu dadi ko mutunci ace an samu mace da zaman gidan yari saboda bashi, mu zama masu kai zuciya nesa da kawar da kai akan abubuwa na rayuwa musamman kayan kyale kyale na zamani, domin da yawa mata abinda ke wahalar damu kenan.

Kafin mu auna cewar zamu nemi bashi mu tabbatar muna da hanyar biya ta yadda ba zamu takura rayuwarmu ba, idan bamu da hanyar biya muyi hakuri mu jira lokaci.

 

[16:28, 9/5/2018] Sister Iyami Jalo: MAFITA

 

1:Mu zama masu kawar da kai a kayan kyale kyalen rayuwa.

2:mu nemi sana’a ta yadda ko da an dauki bashin akwai hanyar biya.

3:kar mace ta dubi rayuwar wata, ta dubi rayuwar ta kawai da abinda zata iya yi.

4:Duk abinda  mace zatayi ya zama ta tsara shi kafin ta fara aiwatarwa.

5: mata mu zama masu godiyar ubangiji a rayuwa.

6:mata mu san cewar duk abinda muka aikata shi ‘ya’yanmu zasu tashi da Shi, saboda haka muyi kokari wurin koyawa yaranmu abubuwa na kwarai.

 

SHAWARA…

Mata mu zama masu wadatar zuci, mu daina biyewa son zuciya, domin shi ke kaimu ga aikata da na sa ni. Abinda maigida Ya kawo mu karba da hannu biyu muyi godiya, mu tsare kawunanmu daga abinda zai jawo mana zubewar mutuncin mu, mu zama masu nema wa kanmu daraja da abinda muka haifa. A k’arshe muji tsoron Allah.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: