Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Matsalolin Auratayya A Yau; Wane Gautan Ne Ba Ja Ba?

by
2 years ago
in NAZARI
4 min read
aure
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

sshinco@yahoo.com

mmeerah@gmail.com.

Aure abu ne da aka saba yi a kowanne jinsi ko nau’i naا halitta (mutane, aljanu da dabbobi), a kowanne addini (Musulunci, Kiristanci, Yahudanci kai har ma da wadanda basu da addinin ma baki ɗaya), sannan kuma a kowacce ƙabila da al’ada. To amma akwai yadda ake nemansa, gudanar da shi ta hanyoyi daban-daban a kowacce al’ada, kabila da addini. Abu mafi muhimmanci dai shi ne, aure abu ne da kusan kowanne addini da al’ada suka yi tarayya a kansa. Hakan kuwa ba zai rasa nasaba da irin dimbin albarka da yawan ni’imomi da suke a cikinsa ba. kamar yadda bincike ya nu na, kusan dukkan kabilu da al’adu na duniya suna daraja tare da martaba aure. Inda gizo ke saka a nan shine, Hausawa suna daya daga cikin kabilun da rigingimun aure da mutuwarsa suka yawaita a cikinta. Watakila hakan ba ya rasa nasaba da irin yanayin zaman auren da shi Bahaushen ya zabawa kansa.

Labarai Masu Nasaba

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

Tushen zaman aure a ko’ina ya kan fara ne daga lokacin da alakar soyayya ta kullu a tsakanin mutum biyu (mace da namiji); domin kuwa irin tarbiyya da ‘training’ da suka bai wa kansu a wannan lokacin, shi zai girmama ya habaka a lokacin da suka yi aure. Idan suka bawa kansu ‘training’ mai kyau, to wannan na nuna cewa za’a samu za aure mai kyau.

Bisa al’ada, akwai irin zaman auratayyar da Bahaushe ya saba da shi, to amma zuwan wannnan zamanin da muke ciki ya kawo canji da dama, tun daga kan neman auren shi kansa har zuwa zaman auren. Bugu da kari, bambancin ra’ayi,tattalin arziki da ilimin zamani duk sun taka rawa wajen canza zaman auren Bahaushe da ma zamantakewarsa ta yau da kullum baki daya.

Wannan shi ya janyo zaman aure iri daban-daban a kasar Hausa, irin zaman da wannan yake yi da matarsa daban da irin wanda wancan ya ke yi da tasa matar, sabanin zamanin baya da za ka ga kusan duk zaman iri daya ne sai dan abin da ba a rasa ba. Wannan kuwa yana faruwa ne saboda dalilai kamar haka:

ADVERTISEMENT
  1. Tattalin arziki a tsakanin Jama’a: yanzu akwai bambancin neman aure da zaman aure tsakanin maikuɗi da Talaka yanzu, koda kuwa a unguwa ɗaya suka taso, ko gida ɗaya da tarbiyya ɗaya, saɓanin zamanin da can baya da za ka ga babu wani bambancin a zo a gani tsakanin auren Talaka da na maikudi.
  2. Wurin Zama Ko Muhalli: idan ma’aurata Hausawa suna zaune a Ƙkasar Hausa misali kamar Kano ko Katsina, to zaman aurensu za kaga ya bambanta da ma’aurata Hausawa da suke zaune a muhallin da bana Hausawa ba, kamar Port Harcourt ko Lagos. Sau tari Bahaushe idan ya tsinci kansa wani da ba irin nasa ba,to yana jefar da al’adarsa ya ɗauki irin ta mutanen da yake a cikin su.
  3. Ilimin Addini ko na Boko: zaman auren Bahaushen da ya yi nisa a ilimin addini da na boko ko ɗaya daga cikinsu, baza a hada shi da na wanda baya da ilimin addini da na boko ba, ko ɗaya daga cikinsu. Bahaushe ko Bahaushiyar da take da isasshen ilimin addini, za ka ga tana kokarin aiki da koyarwar addini fiye da ta al’ada a cikin zaman aure ko a lokacin yin sa. Komai zasu yi to zasu yi ne ta hanyar da addinin Musulunci ya koyar.
  4. Halayya Irin Ta Ɗan Adam: Yanayin halayar mutum yana taka muhimmiyar rawa a dukk abinda zai aikata. Da yawa daga cikin al’ummar Hausawa, zaman aurensu ya kan ginu a kan irin halayyarsu. Yayin da Bahaushe da Matarsa suka mori halayya mai kyau da mu’amala mai nagarta, to zaman aurensu kan kasance mai inganci. Idan kuwa halayyarsu marasa kyau ce musamman idan aka yi gamo da rashin tarbiyya, to kullum sai dai kaji matsaloli a cikin zaman aurensu. Wani lokacin ba a taruwa a zama daya, za kaga mijin ya more hali mai kyau da tarbiyya amma matarsa sai a hankali, to a nan abin ya kan zo da sauki tunda shi mijin ba shi da matsala,kuma shine shugaba.

Duk da cewan kusan kowa ya san wadanan dalilai dana bayar a sama,amma hakan bai hana mazan da mata nunawa juna yatsa da sunan dayan ne keda laifi ba idan aka samu matsala a zama irin na aure. A iya binciken da nayi wannan sune korafe-korafen da mazan Hausawa ke yi game da matan su,kuma suna ganin idan matan suka gyara zaman nasu zai inganta:

  1. RAINI: An yi kiyasi cewar akwai tsabar raini ga matar malam Bahaushe,zaka iya zama da mace shekara da shekaru amma rana daya matsala ta samu, za ka ji maganganu na raini. Ka ji suna cewa mazajensu kaddara ce ta saka suka aure su, ko kuma Idan ba kaddara ba; ba abunda zai sa na aureka,ai namiji ba dan goyo bane,daman duk wacce ta dauki namiji uba za ta mutu marainiya da dai sauran kalamai irin wanan.
  2. RASHIN IYA YIWA MIJI HIDIMA: A nan ma za ka ga sauran matan kabilu suna yi wa mazajensu wanki da guga da wanke takalmi da lura da kwalliyar maigida da gyara masa ado, wasu har gona suke zuwa taya mazan aiki, daukar nauyin karatun ‘ya’ya da sauransu. Amma matan bahaushe babu ruwansu, sai dai su ci su kwanta, babu ruwansu da mijinsu, balantana su yi masa wata hidima,sai dai bani-bani.
  3. RASHIN GODIYA: Matar Bahaushe tana da wata al’ada ta rashin godewa kokarin da mijin ta yake mata. Ba su nuna godiyar a aikace ko kuma su furta da baki. Akwai matan da suke cewa mazajensu mai suka taba yi musu tunda suka aure su “WANNAN KALMA CE MAI MUNI”. Daruruwan shekarun da suka gabata ANNABI (S) ya siffanta mata masu irin wannan dabi’a, amma abin mamakin shi ne yadda kasan da matan Hausawa Annabi (S) ya ke don bincike ya nuna sun fi sauran mata fadarta.
  4. BOYE SOYAYYA GA MIJI: ita ma wanan wata dabi’a ce ta matan Hausawa, rashin nunawa miji soyayya sai dai baya-baya, dan wasu matan sun dauka nunawa miji soyayya nasa miji ya rainaki ko yace miki ‘yar iska. Wannan ma sai ya sa kaga ba a yi masa komai. SU MATAN HAUSAWA ABINDA SUKA DAUKA NUNA SOYAYYA GA MIJI ITA CE KAWAI KWANCIYAR AURE, bayan haka ba wata soyayya da suke nunawa mazajensu (ita kanta wasu mazan na korafi da rashin iyawa), sau tari za ka ji matan wasu kabilun suna cewa “Wallahi da za su hada kishi da Bahaushiya sai sun kwace mijin, ba malamai ba boka kawai tsantsar nunawa miji kulawa da soyayya da hidima”ce za su yi amfani da ita.

Za mu cigaba a mako mai zuwa inshaAllah.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Waiwaye Da Tsokaci Kan Matsalolin Shaye-Shaye A Tsakani Matasa

Next Post

Tabarbarewar Tsaro a Nijeriya: Nazari Da Tsokaci Daga Littafin Bukar Usman

Labarai Masu Nasaba

Dariye Da Nyame

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

by Idris Aliyu Daudawa
1 month ago
0

...

Bangaranci

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

by Muhammad Maitela
2 months ago
0

...

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

by
3 months ago
0

...

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

by
7 months ago
0

...

Next Post
Kabilanci Da Son Kai Sun Kassara Mu

Tabarbarewar Tsaro a Nijeriya: Nazari Da Tsokaci Daga Littafin Bukar Usman

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: