Matsalolin Biyan Albashi A Jihar Bauchi Sun Kawo Karshe, Inji Hon. Zaki

Albashi

Daga Khalid Idris Doya,

Kwamishina mai kula da lamuran kananan hukumomi da masarautu a jihar Bauchi, Hon. Abdulrazaz Nuhu Zaki ya bayar da tabbacin cewar, matsalolin biyan albashin ma’aikatan gwamnatin jihar da na ‘yan fansho da a baya ya zama daurin gwarmai yanzu ya kawo karshe.

Hon. Abdulrazaz Nuhu Zaki da yake yin hira da manema labarai a Bauchi kan wannan batu, ya bayyana cewar, albashin ma’aikata na wata-wata, na kuma watan Mayu na wannan shekara za a biya ba tare da an dakile shi ba, yana mai cewar, ba wani ma’aikaci na gwamnati da zai yi kukan ba a ba shi albashin watan Mayu ba.

Ya bayyana cewar, ma’aikatan gwamnati wadanda a wata daya ko biyu da suka gabata da aka tsaida biyan albashin su kimanin mutum dari bakwai da goma sha-biyar (715) duka an tantance su, kuma an samu ma’aikata kimanin dari biyar da arba’in (540) daga cikin wadancan adadi duk ma’aikata ne na zahiru bana bogi ba.

“Maigidan mu gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, Kauran Bauchi da ya fahimci akwai nuku-nuku a cikin biyan albashin ma’aika, ya ce ya nada mukaddashin sa Sanata Baba Tela ya jagoranci matsalar warware matsalolin biyan albashin ma’aikata a jihar nan”.

“Kuma Allah da Ikon Sa, Mukaddashin Gwamna da aka daura masa wannan nauyi, sai ya yi bashirar kafa karamin kwamiti a karkashin nasa babban, sai ya sanya ni na jagoranci karamin kwamiti wanda aka ba shi nauyin lamuran kananan hukumomi. Dama ina Allah ya kawo ranar da za a bani wannan aikin, mu kawo karshen wannan dambarwa. Bangaren ma’aikatan jiha kuma aka baiwa shugabancin su wa shugaban ma’aikatan jiha”.

Zaki ya bayyana cewar, a cikin kwanaki goma suka tantance ma’aikata na bangaren su, yayin da suka yi aikin tantancewa na gaskiya na fanni-fani kuma aka baje komai akan faifai a tsakanin ‘yan kwamiti kuma suka tsara komai daki-daki yadda ya dace.

Kwamishina Nuhu Zaki ya bayyana cewar, akwai mutum 554 a bangaren ma’aikatan kananan hukumomi wadanda duk sun tantance su, suke fitar dana kirki dana jebu dabam-dabam, yana mai bayar da tabbacin cewar, albashin watan Mayu babu wani ma’aikata daya tilo da za a ketare wajen biyan albashi.

Ya ce, “Da yardar Allah wannan karo, babu wani ma’aikacin gwamnati, na jiha ne ko na kananan hukumomi da za a ketare shi wajen biyan albashi,” ya kara da cewar, babu wani lokaci tunda suka kama ragamur mulki wani ya yi masu boren cewa ba a biya albashi ba.

“Mun tantance, mun gyara, mun fidda na ainihin, mun kuma cire na bogi. Akwai wadansu wadanda na gaskiya ne, amma ba a biyan su, don haka yanzu mun fayyace na gaskira dana bogi, domin muna so kowa ya karbi hakkin sa. Mai girma gwamnan Bauchi kullum yana jin bacin rai, yana jin bakin ciki ace ma’aikaci wata ya kare bai samu albashinsa ba.

Zaki ya ce yanzu da Allah ya Kawo karshen lamari, kuma magana ta zama kurumkus, yana mai cewar, mun jagoranci warware wannan lamari kuma Allah ya kawo karshen sa. “Kuma an samu jinkirin biyan albashin ne saboda mun ja dag aba za a biya da tsohon bauca ba”, inji shi.

“A cikin tacewa da muka yi, mun samu wasu ma’aikata sun tafi ne ba a san inda suke ba, wasu kuma sun tafi aiki  aro a wani wuri, wadanda bai kamata sunayen su yana fita a cikin jadawalin masu karban albashi ba. Akwai ma wadanda ba a san ko su wanene ba su, akwai wadanda tun-tuni suka bar aiki amma suna karban albashi, wadansu ma sun mutu, amma suna cikin masu karban albashi”.

Exit mobile version