Idris Aliyu Daudawa" />

Matsalolin Cutar Tamowa Da Yadda Za A Nisance Ta

Tamowa idan aka yi la’akari da ita ma’anar wannan cuta ce wadda al’umma suke ko kuma kananan yara suke kamuwa da ita, sanadiyar rashin isasshen abincin ci, musammam ga kananan yara. Wannan matsala tana faruwa ne a yawan-yawan lokaci ga kasashe ma su fama da matsalar rashin kayayyakin abinci na yara, wadanda suka kamata su ci. Wannan cuta ana iya samunta a kasashe irin Amurka da kuma wasu kasashen da suke da kayayyakin abinci masu yawa. Amma an fi samun irin shi wannan al’amari a a sahara a Afirka.

Mafi yawan yara da kuma sauran wakanda suka kamu da wannan matsala ta Tamowa suna samun waraka wato suna samun sauki sosai,. kamar ma basu taba yin ita cfutar ba. Amma kuma wannan abin bah aka nan yak an tafi ba salun alun, sai idan har an bi tsarin da aka shardanta masu muhimmanci, musamman cin abubuwa da za su gina masu jiki da samar ta amfanin abinci masu kyau da suka dace. Yaran da suke da Tamowa  ba su girma kamar yadda tsararrakin su suke, domin za su tsumbure ne kawai. Saboda haka shi rashin kulawa da al’amarin yana jefa su cikin wahala matuka, in aka yi jinkiri wajen magance shi. Tamowa na  samar da illa da kuma babbar  barazana ga lafiya in ba a kula ba cikin sauri, domin yana iya karya wasu sassan jikin yara  masu amfani ga rayuwarsu,  daga karshe kuma su kai ga mutuwa.

 

Me ke haifar da Tamowa?

Akwai abubuwa da dama da suke haifar da Tamowa amma muhimmi daga ciki shi ne abinci da zai gina jiki. Kowa na bukatar abubuwan da za su gina jiki domin wasu kwayoyin halitar jikin dan adam su sami inganci. Duk jiki da ya samu isasshen abincin da ke gina jiki yana dada farfado da wasu kwayoyin halitta  (cells) da suka raunana. Ana bukatar irin waɗannan sinadaran ga jarirai da kuma masu dauke da juna biyu don samar da lafiya. Amma rashin samun sun a haifar da Tamowa.

Alamomin Tamowa sun hada da:

Canji da ga launin fatar jiki da gashi (tsatsa-tsatsa)

Gajiya

Zawo/gudawa

Rashin karfin jijiyoyin jiki

Rashin girma da nauyi

Kumburin  idon kafa  da rumfar kafa da kuma ciki

Lalacewar kwayoyin halitta wadanda suke kare mutum daga kamuwa da cuta, wannan kuma shi zai iya sa matsalar ta kara yin kamari.

yawan kurarraji a jiki

gigicewar yaro

 

Yadda ake gane asalin Tamowa:

Muddindai ana tunanin cewar cutar Tamowa ce,  da farko shi Likita zai yi nazari ya duba yadda hantar wanda ake tunanin hakan gare shi, wato ya kamu da ita cutar, da kuma yadda hantar ta kumbura,bayannan kuma sai a yi gwajin fitsari da kuma jini domin a ga yadda yawan abinci da ke gina jiki yake a jikin yaron a cikin jinansa. Sai kuma a duba yanayin cin abincin yaron, da dai sauran makamantan su.

 

Yadda ake magance Tamowa:

Ana magance Tamowa ne ta hanyar cin abinci masu gina jiki musamman ma lokacin da aka fahimci cutar ta darsu a jikin mutum. Sannan sai a mayar da hankali kan abubuwa da za su taimaka wajen inganta karfin jiki.

Matsalar da cutar Tamowa ke haifarwa tana da yawa, da zarar  kuma mutum ya shiga cikinta, manufa ya kamu da ita, to da wuya ya cimma tsararrakin shi, wajen girma, domin kuwa duk tsararrakinn shi da ma wadanda suke kasa da shi  za su tsere mashi da tsarin kirar jiki da kuma girman kashi.

 

Za a yi maganin cutar ne  ta amfani da wadannan abubuwan kamar haka:

cin abincin teku

cin kwai

cin nama

cin wake

cin ‘ya’yan itatuwa da dai sauran makamantan su.

Exit mobile version