Zubewar ciki ko wanda aka yi da gangan ko wanda ya zo saboda wani dalili, akwai abubuwa na ruda kai da suke zuwa bayan yin sa wadanda wasu suke tafiya da kansu ba tare da an sha magani ba wasu kuma sai an sha magani ko an dauki wani matakin.
1-Infection na daya daga cikin matsalolin da zubewar ciki yake haifarwa kamar inda akwai sauran tsoka da ta rage a cikin mahaifa bayan zubar da cikin. Sannan wani lokacin idan an yi amfani da wasu abubuwa wajen zubar da cikin kuma suna iya haifar da kwayoyin cuta ga mahaifa. Idan mace ta samu irin wannan musamman Idan ta samu wasu alamomi kamar haka
- i) Zafin jikin ta watau temperature ta yakai 38oc.ii) Yawan bugun ziciya kamar ya buga sau dari cikin minti daya.iii) Kumburin ciki, ciwon ciki, taurin ciki.ib) Idan ruwa mai wari yana fita ta bagina.b) Jin rashin lafiya ko gajiya sosai.
To idan infection ya samu wadda tayi barin ciki ko zubar da ciki a irin yanayin, wannan bazai tafi ba har sai an tabbatarda ancire abinda yayi saura a cikin.
- i) Kodai shi ma akwai sauran wata tsoka data rage a cikin mahaifar bata gama fita ba.ii) Ko kuma idan anyi amfani da wasu abubuwa yayin zubar da cikin kila anji ciwo a wani wurin.iii) Kokuma kila bakin mahaifa ko mahaifar takamu da infection. Saidai a sani idan akwai sauran wani abu daya rage a mahaifa to wannan infection din kokuma bleeding din bazai tafiba harsai an fitar da abinda yarage a cikin mahaifar.
3- Akwai matsalar kumburin ciki, ciki zai kumbura sosai kamar Akwai ciki wata hudu. Wani lokacin cikin yana tafiya da kansa, musamman idan ba wasu matsaloli dayawa, amma wani lokacin cikin na daukar wasu watanni kafin yatafi amma ana samun wasu matan sukai har wasu shekaru ma yana kumbura akai akai wanda dukkannin wadannan matsaloli ciki bazai shiga ba harsai an magance su. Akwai wasu matan kuma da jinin al’adarsu yakan dauke zuwa wasu kwanaki masu yawa, wasu kuma har zuwa wasu watanni ma ko shekara ko shekaru wasu kuma sai aga yana wasa sosai.
Duk wannan wani lokaci jiki ba shi da bukatar wani treatment, zai koma a hankali kamar yadda yake a baya.
4- Wasu matan kuma za aga insukayi barin ciki yan kwanaki kasa da sati daya zasuyi bleeding kawai amma bayan sati biyu saiya dawo da karfi kokuma wasu matan suyi bleeding sati daya zuwa sati biyu bayan yadauke da kwanaki kadan sai su ga wani, to in suka lura ba jinin zubar cikin bane, a’a, spotting ne wanda nasha yin magana kansa. Wasu kuma sukan wuce sati biyu suna bleeding, idan wannan bleeding din yazo da ciwon mara sosai, fitar jini sosai misali duk bayan awa daya zuwa biyu a rika canza pads, ko jiri, ko gani bishi bishi ko jikin mutum yayi weak sosai kokuma jinin yana fita da clots duk wadannan yana bukatar aje asibiti amma kafin haka mace da ta ke bleeding musamman da zubewar ciki sai asamu abinci masu sinadarin iron ko iron supplements tarika amfani da su sannan kuma a samu hutu.