Mustapha Ibrahim">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Matsalolin Da Su Ke Durkusar Da Kasuwanci A Kano -JIFATU

by Mustapha Ibrahim
December 19, 2020
in LABARAI
4 min read
JIFATU
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Shugaban rukunin kamfanin Jifatu na kasa, Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad, wanda aka fi sani da JIFATU, wanda babban ofishin sa ke Kano, ya bayyana cewa, babban dalilin da ke durkusar da kasuwanci da `yan kasuwar Kano shi ne dogaro ko tsayawa akan hanya daya tak, wanda yanzu zamani ya zo an wuce wannan tsarin kasuwanci a Duniya.

Don haka sai ya bayyana cewa akwai bukatar a fahimci hakan kuma a gyara domin ci gaban kasuwancin Kano da kasa baki daya. Ya ce, ko a Legas ba sa kan hanya daya ta kasuwanci kamar Kano da wasu jihohin Arewa abin ya yi naso na tsayawa ko dogaro da hanya daya.

samndaads

Alhaji Sabitu Yahaya ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na kasa NTA da ke Kano, a cikin wani shiri da su ka gayyaci dan kasuwar a ranar Asabar da ta gabata.

Inda ya tabo al’amura da su ke kawo cikas a kasuwa da kasuwanci da kuma abubawan da suka dabaibaye ‘yan kasuwa a Kano dama kasar baki daya.

Don haka dan kasuwar ya bayyana cewa yanzu duniya ce ta canji da ke bukatar fadada tunani da fadada kasuwanci, musamman ita Kano da ake mata kirarin kasuwanci, to dole ne ya zamana an zamanatar  da kasuwancin kamar yadda bahaushe ke cewa sana’a Goma Maganin mai Gasa, gida Biyu maganin Gobara.

Alhaji Jifatu ya kuma bayyana cewawani abu da ke inganta kasuwanci,  gaskiya da rikon amana da kuma barin hassada a harkar kasuwa, dole kuma a guji abin da turawa suke cewa ‘one line business’, shaharar Kano da kasuwancin duniya sun wuce wannan layin a yanzu.

Ya ci gaba da cewa, harkar ci gaban al`umma a yanzu na da bukatar Sarakunan mu na Gargajiya su waiwayi aikin kakannin su na shekara sama da 200 da su ka wuce su ga sun yi aiki irin na su to idan ba su yi ba to dole su yi aiki irin na su na kyakkyawan shugabanci nagari kamar yadda ya hau  kan ko wanne shugaban a wannan lokaci.

Ya ce haka su ma Malaman mu dole ne su sauke nauyin da ya hau kansu ta hanyar fadar gaskiya komai dacinta kuma dole duk wanda zai fadakar wajibi ne ya sa cigaban al’umma a ransa ba tare da sanya san zuciya ko sanya siyasar Addini ba ko kuma ci da Addini.

Domin Malami mutum ne mai daraja, dan haka ma ake cewa malamai magada Annabawa, gadon Annabawa shi ne Ilimi, gaskiya, tsoran Allah da jajircewa.  Wajibi ne malamai su jagoranci jama’a ta hanyar koyi da magabatan mu da ake yabo ako da yaushe.

Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad Jifatu.jpg 12

Su kansu shugabannin da al’umma baki daya akwai bukatar zabo mutane a kowanne yanki Shida da ke Nijeriya wadanda aka yadda Amanar su Gaskiyar su da Mutumcin su su na fifita shi akan cigaban Alummar su da kasar su akan kare siyasar su da kabilar su wato adalcin su da Gaskiyar su ta fifita akan komai to irin wadannan mutane da suka hada da malamai, sarakuna, malaman Jami'o'i,yan kasuwa, Manoma da sauran su duk wanda zai ba da gudummawa wadanda aka san amintattu ne a cikin Alumma a basu dama su zo su shiryawa kasar nan <strong>Manhaja</strong> ta shekara sama da 300 mai zuwa domin cigaban Alumma mai zuwa nan gaba kuma hakan ya kasance duk wani shugaba da ya zo akan ta zai dora babu maganar wata jamiyyace ke mulki ba jamiyya kaza ce ke mulki ba, wannan shi ne irin yadda kasashin duniya ke yi wajan ciyar da Al`ummar su gaba musamman kasashi irin su Rasha da irin Tsare Tsaran su abu ne da dole a kasa kowa yasan matsayin kasar sa da kuma irin gudummawar da zai bayar.

Haka kuma don ga ne da rashin aikin yi kuwa da matasa suke fama dashi a kasar nan, ya ce su a tsarin tafi da Jifatu kowa, akwai abubuwa da su ke yi wanda yake samawa mutane da ba, a san iya karsu ba aikin yi musamman idan kai laakari da irin abubuwan da suke sarrafawa da kuma zamanar tarda shi, kuma tunda kakan masanaantar shinkafa, Alkama, Masara, Gero, Dawa, Rogo, Goriba, Manshanu, dadai sauran su wadanda ke bawa, ga kuma tsarin mu na samawa mata sanaa ta hayar sasu su yi abubuwa kamar irinsu zobo, Aya, ridi, Kantu, kolikoli, Cincin, kukan maya, kubewa, kabewa, aleyawu, Tomatur, larkashi, da sauran sanaoi masu albarka da ake ganin kamar kanana ne, wanda ni kaina da aka gaya ceni Legas, bude kamfanin cincin ina dawowa Gida na umarci iyalina da su samar da irin wadanan abubuwan wanda duk suna cikin Jifatu don dai asamawa al`umma aikin yi da kuma daraja namu na gida.

Jifatu ya ce, yanzu haka sunzo da tsarin cin kasuwa awa 24 a duk shagunan su wanan kuma anyishi ne dumun canza fasalin kasuwa domun dai hakan zai sa a kara yawan maikata da saukaka jama hada hada kuma ya kawar da tsoro a zukatan aluma. Talafin ilimi ya ce, bashaka rukunonin Jifatu na da Gidauniya ta talafin Ilimi tun daga kan daliban makarantun firamare, sakandire, kwalejujin Ilimi da na kimiya da fasaha harzuwa jamioin  Gida da makarantun waje da Jifatu ke yi domun bonkasa Ilimi haka kuma akwai tsarin talafawa harkar Lafiya ga aluma marasa karfi kamar yadda ta kamata a wanan lokaci

A karshe Alhaji Sabitu Yahaya Muhammad Jifatu ya bayana cewa, akwai bukatar ‘yan Nijeriya sun hada kansu ta hanyar yin laakari da nagartar motun ba kabilarssa ba ko kungiyar da yake ciki ba domun ko da Addine ne mutum ya ke yi to Addini na Allah ne kuma mutum kansa ya ke yiwa babu bukatar neman daukakar Duniya da Addini wanan shi ya kamata kowa ya tsaya a kai tunda dama can Allah ya hana ci da addani kuma wajibi ne shugabani su tashi tsaye wajen gyara kowa tun daga kansa zuwa na kusa da shi zuwa unguwar da kake da garinku da karamar hukumarku da Jaharku da kasarku kuma gyara baya yiwuwa sai an batawa janma rai musamam masu san zuciya da rashin kishin aluma da kasa to indai za ai gyara tu dole a ajiye san zuciya a fuskanci gaskiya komai dacinta domin ci gaban alummar Nijeriya.

SendShareTweetShare
Previous Post

Wajibi Ne Mu Hada Hannu Wajen Yaki Da Rashawa- PACAC

Next Post

Nijeriya Ta Tsara Shekaru Biyar Don Magance Matsalar Yunwa

RelatedPosts

Sheik Karibullah

Sheik Karibullah Ya Nada Alhaji Kabiru Sani Kwangila Khadimul Nabiyya A Taron Maulidin Gidansa

by Mustapha Ibrahim
9 mins ago
0

A ranar Lahadi ne aka gudanar da Maulidin Manzon Allah...

Magance Matsalar Tsaro

In Dai PDP Na Son Samun Nasara, To Ta Sa Mata A Gaba – Amina Soba

by Mustapha Ibrahim
14 mins ago
0

Hajiya Amina Adamu Soba, Tsohuwar 'yar takara ce a jam'iyyar...

Allurar Rigakafin Kurona

An Yi Kira Ga ‘Yan Nijeriya Da Su Rungumi Allurar Rigakafin Kurona Da Zarar An Fara

by Mustapha Ibrahim
19 mins ago
0

An yi kira ga al"umar kasar nan su yi amfani...

Next Post
Magance Matsalar Yunwa

Nijeriya Ta Tsara Shekaru Biyar Don Magance Matsalar Yunwa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version