Rahama Abdulmajid" />

‘Matsalolin Da Za Su Ci Gaba Da Rayuwa A Arewa Nan Da Shekara 2040 Matukar…’

Nazari kan wasu daga munanan al’amurra da ke addabar Arewa da babu wata taswira ta yi musu gyara na dindindin su ne:

1 Hauhawan jahilci tsakanin matasa

Shekaru 20 baya ba gagara tallafin ilmin zamani yayi wa Arewa ba, bata kammala amincewa da Shi bane. Sai dai a yanzu da ta kammala amincewar an sami hauhawar haihuwan Yaran da iyayensu ba zasu iya basu ingantaccen ilmi ba. A yayinda talakan da ke da karfin bayar da ilmi ga yara 3 ya haifi yara 10, akwai yiwuwar daya ne tal zai iya samin ilmin yayinda ragowar tallafin ilmin na mutum biyun zai dulmiye a kudin cefanen abinci kenan a tsakanin iyaye talakawa goma zasu iya samar da jahilan matasa akalla guda 90 Wanda zasu zamo nauyi ga shekara 21 masu zuwa- Akwai sakamakon bincike akan hakan-

2 Kyamar Jahilci

A yayinda duniya ta dunkule ta koma cikin wayar hannu da ba a iya sarrafawa sai da ilimin rubutu da karatu na wasu manyan yarukan duniya har ta kai a manyan Birane daga cefane, tasi, har me kwasan shara akwai manhajar da aka tanada a waya don kiransa ya zo har kofar gida don biya maka bukata. Nan da shekara 20 zai yi wuya a sami wani gurbi da zai saura don yin hulda da jahili. Wannan na nufin akasarin yan cirani dake yin hijira zuwa alkarya don yin wasu aiyuka da aka sauwake wa jahilci su ma zasu fara rasa hurabensu. Misali a garin Abuja samfurin motocin Uber da tedify sun tilastawa daruruwan direbobi yan cirani rasa aiyukansu sakamakon kasa iya sarrafa manhajar Uber din akan wayoyinsu saboda rashin karatu ko yaya duk kuwa direbobin yan cirani sukan fi saukin kudi da sanin hanya, Amma basu da saukin samu akan wayar hannu ta zamani.

3. Rashin aikin yi.

Rashin aikin yi na iya nunkuwa a Arewa duba da yadda gwamnatin Arewa ta kasa samar da guraben aiyuka ga matasa ko basu dalilan iya kirkirar aiyuka ta hanyar wadata yankin da wutan lantarki, da ruwan sha da ilmi mai rahusa, maimakon yin hakan Gwamnatocin sun fi mai da hankali ga gina ababen da zasu baiwa dan Arewa damar sake zabensu maimakon gina dan Arewa, misali gina gadoji da manyan tituna da bayar da kudin cefane na babu gaira babu dalili a matsayin jarin da ba a tanadi wajen juya shi ba. Ko kuma baiwa mata tulunyar suyan kosai da ba zata gaza yin tsatsa ba nan da shekaru2 masu zuwa. Tare da tilasta Dan Arewa yayi noma ba tare da wani ingantaccen shirin noma ba

Wannan lamari ba za a gane illarsa sai gwamnati ta bar Arewa zuwa kudu nan da shekara 4 in Da akwai yiwuwar bazata dawo ba sai bayan wasu shekaru 16 wato dai nan da shekara 20 bayan ciwon ya rika.

4. Matsalolin Al’umma

Kasawar malamai da masu fada aji wajen dakile matsalar mace-macen aure dake yin illa ga tarbiyar yara fiye da illar da yake yiwa maauratan, da matsalar Almajirci da yakinta ke samin tarnaki ko dai daga kungiyoyi masu ci da gumin almajirai, ko gidajen malaman da ke daurewa almajircin gindi saboda suna da maslaharsu a ciki ko no kuma daidaikun mutane da ke amfana da almajiran wajen aiyukan gidansu cikin sauki ko ma uwa uba iyayen da ke yin cikin almajiran su haifa su turo su bara ba tare da an sami hanyar dakatar  dasu ba.  Wannan da ma wasu dalilai da suka hada da mace macen iyaye a dalilin rashin tsaro ko rashin ingantaccen kiwon lafiya zasu sake ninka Yaran da basu sami tarbiyar iyaye ba a Arewa a dalilin ko dai mutuwar aure ko mutuwar iyaye ko hijirar yara daga gaban iyaye wanda nan da shekaru 20 ragamar raino zata iya shiga hannun wadanda basu sami raino ba Da kaso 45 cikin dari ( Bincike ne)

5. Matsalar Muhalli

Sama da shekaru 30 kenan akasarin yan Najeriya musamman ma yan Arewa suka hakura da samin kashi 70 daga moriyar Gwamnati ta hanyar ruwa da wutan lantarki inda neman ruwa da fetur ya shiga lissafin ababen da suka hana dan Najeriya kishin gwamnatocinsa ko ganin mutuncinsu saboda kasa share masa hawaye da suke a wannan fannin da ya fi kowa.

Exit mobile version