Matsalolin Malaman Hausa A Makarantu Masu Zaman Kansu

Koyarwa da harshen gado ko harshen uwa (kamar yadda wasu ke fada) ya kasance ginshikin cigaban duk wani fanni na rayuwa, musamman a wannan zamani da kimiyya da fasaha ke taka rawar gani.

A dokar Nijeriya, an amince a wani mataki na firamare a koyar da yaro da harshensa na gado, sai dai bisa la’akari da yawan harsunan da muke da su aka zabi Harsunan Hausa, Ibo da Yarbanci su zama wadanda za a yi amfani da su bisa la’akari bazuwar harsunan a manyan yankunan kasar.

Magabatan shugabanni na farko a jamhuriya ta farko, sun yi tsayuwar daka kan wannan, amma a wannan zamanin koyarwa da harshen gado ya zama abin dariya har ma ya zama daya daga cikin dalilin kaurace wa makarantun gwamnati zuwa makarantu masu zaman kansu.

Wannan ya sa muka kawo maku wata mukala da wani Malamin Hausa, Ish’ak Idris Guibi ya taba rubutawa a shekara 23 da suka gabata, kan matsalolin da malaman Hausa ke fuskanta a makarantu masu zaman kansu domin sake waiwayar matsalar da nufin gyara.

Harshen Hausa

Harshen Hausa na daya daga cikin manyan Harsuna da ake amfani da su, ba a Afirka kadai ba, har ma a kasashen da suke tinkaho a yau cewa su ne masu fada a ji a duk duniya. A kokarin Nijeriya na kamo sahun wadannan kasashe masu tinkahon fada a ji ne, wato ta fannin siyasa, da kimiyyya da fasaha, sannan uwa-uba, ta fannin tattalin arziki, ya sa aka tilasta wa dalibai koyon manyan harsunanmu na kasa, wato Hausa da Ibo, da Yarbanci, a kwalejojinmu, da makarantunmu na sakandare, tun ba ma kwalejojin tarayya ba. Domin duk kwalejin gwamnatin tarayya da ka zaga a kasar a yau, za ka tarar cewa akwai kwararrun malaman nan uku da aka tanada don koyar da harsunan namu uku na kasa. Su kuma dalibai, in an ce yaro gaba da baya bahaushe ne, za a tilasta masa, ya koyi Hausa, sannan ya koyi ko dai harshen Ibo, ko Yarbanci. Kazalika, idan yaro gaba da bayansa dan Ibo ne, za a tilasta masa, ya koyi Ibo, da ko Hausa, ko ya hada Ibo da Yarbanci. Haka ma dan Bayarabe, dole ne ya koyi yadda ake nazarin Yarbanci, da ko Hausa, ko ya hada Yarbanci da Ibo. Sannan kowanne yana da Manhajarsa daban. Misali Manhajar da za ka yi amfani da ita wajen koya wa wanda, gaba da bayansa,  bahaushe ne, daban da wanda za ka koya wa dan bayerabe, ko dan Inyamuri wato Ibo, da ba su san ko zo in kashe ka ba a Hausa.

Hausa A Makarantun Sakandare Masu Zaman Kansu

Idan ka leka makarantun sakandare masu zaman kansu da ke Arewacin kasar nan kuwa,  za ka tarar da cewa akwai Malamin Hausa ne kawai kwaya daya tal. Irin wadannan makarantun, za ka tarar cewa in ma akwai ‘ya’yan Hausawan, to fa ‘yan kalilan ne. Saboda haka, maimakon a bar malamin Hausan ya bi tsarin da na zayyana a baya, wato irin tsarin kwalejojin gwamnatin tarayya, sai a ce wa Malamin ya dauka kowanne yaro gaba da bayansa bahaushe ne. Saboda haka, Malamin ya yi amfani da Manhajar da ake koya wa wanda ya san zo in kashe ka. A saboda haka sai Malamin ya kwashe shekaru yana koya ma yara wanda a karshe, ka samu cewa yaran ba su san inda aka nufa ba. A yi jarabawa, a karshe duk yaran su zube. Ka ga ba laifin iyaye ba, ba laifin Malami ba, kuma ba laifin yaro. Sannan ba dan karamin wulakanci ake nuna wa Malaman Hausa a irin wadannan makarantu ba. Ga mai son saninsu ga ‘yan misalai. Na farko kai Malamin Hausa, kai kadai za a danka wa tun daga ‘yan aji daya, har zuwa ‘yan aji shida, wai da sunan ka koya musu Hausa. Ga jakin Kano ya iso. Abu na biyu, sai ka koya wa yaro Hausa tun yana aji daya, sai ya kai aji hudu, sai ya kira babansa da sunan cewa shi fa, ya gaji da Hausar. Wani lokaci makarantar ce ke ba da umarni bayan ka koyar da yaron gaba da bayansa bahaushe ne wato tun daga aji daya, har aji shidansa, sai a kawo umarnin cewa in ya ga dama ya rubuta ta a jarabawarsa ta fita. In bai ga dama ba, ya watsar da Hausar. Wani abin ban haushi, shi ne irin wadannan Malaman Hausa, su ake biya albashi dan kankani wai saboda darajar mai koyar da Hausa ba ta kai ta masu koyar da sauran fannonin ba. Sannan har ila yau, da gangan in an zo shirya jarabawa a irin wadannan makarantu, sai a sa jarabawar Hausa a karashe wato bayan an gama kowacce jarabawa, sai a ce ai keken rubutu ya lalace, ko kuma an buga jarabawar Hausar, amma kafin a bai wa yara su zana jarabawar, sai a nemi taimaka wa dalibai satar jarabawa. Idan Malami ya ki ba da hadin kai, a buga masa sharri a kore shi. Wata matsalar kuma da Hausa ke fuskanta a irin wadannan makarantun masu zaman kansu, ita ce idan an zo bikin yaye dalibai duk yara da suka yi fice a fannin harshen Hausa, sai a kudundune kyautar da za a ba su a cikin takardar kunshe kosai da tsire, amma sauran fannonin sai a sami leda mai tsada da kyalli a kudundune kyautar a ciki a ba su. In ana kara wa malamai girma kuwa, sai a ki kara wa Malamin Hausa. Saboda wai in ana maganar malamai, shi ai ba zai tsoma baki ba. Wai mene ne ke da wuya a cikin Hausar? Magana ta karshe ita ce in aka kasa makarantun da ke zaman kansu a kasar nan, cikin kashi goma, kashi biyu ne kawai suke daukar malaman Hausa don koyar da Hausar. Kai malamin Hausa, ko ka cusa kanka cikin irin wadannan makarantu, tursasawa ya sa ka bar wajen.

Shawara a nan, ya kamata, daukar malaman da za su koyar da wadannan harsunan namu uku, ta zama sharadi na farko kafin a ba da izinin bude irin wadannan makarantu masu zaman kansu. Kuma ya kamata ma’aikatar ilimi, ta cire kunya, ta dinga sa ido a kan irin wadannan makarantu. Don kuwa akwai irin wainar da ake yawan toyawa da ba su lissafatuwa.

Kammalawa

Wannan Makala ta zayyano wasu da daga cikin dinbin matsalolin da malaman da ke koyar da Hausa a wancan zamani (shekarar 1994) suka fuskanta a makarantun da ke zaman kansu. Sai dai ban sani ba ko har yanzun wadannan matsaloli suna nan ko sun kau?

Is’hak Idris Guibi

Malami a Sashen Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Kaduna.

guibi14@yahoo.com

08023703754

Exit mobile version