Masoya na da matsaloli da dama a wannan lokaci wanda ba za su lissafu ba sai dai a tsakuro kadan, daga cikinsu akwai matsalar Son Maso Wani ta Hausawa su kan ce Koshin wahala.
Namiji yakan so wadda yake so amma kuma ita ba ta son shi, wanda wannan ya zama ruwan dare gama duniya tsakanin masoya, wanda hakan ba ya tsaya iya kan maza ne kawai ba har ma matan.
A kan samu mace tana son namiji kamar me, za ta ji duk duniya babu wanda take so face wannan nan wanda ya shiga cikin zuciyarta, baccinta ma da tunaninsa take kwantawa haka ma tashin ta yake kasancewa a kullum.
Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, duk da wannan son da take masa in ta sanar da shi ba zai karbi soyayyarta ba, domin shi ta shi zuciyar babu sonta a ciki son wata ne a cikin tasa.
Abin duba wa anan shi ne a yayin da namiji ya ji baya son wannan wadda take sonsa ko kuma ita ta ji ba ta son wanda yake sonta maimakon a rabu lafiya da juna a lallami juna cikin salama sai kuma a tashi da bacin rai cikin zuciyar kowanne dayan ciki.
Masoyan sukan nunawa masoyan nasu wanda ba sa so kiyayya karara maimakon a ba wa juna hakuri tun a farkon da dayan ya sanar da wanda yake so muddin ya ji baya sonsa, a’a sai dai kai tsaye a sanar wa da masoyin cewa ni fa ba na sonka ko kuma ba na sonki, wannan yana daya daga cikin matsalar da masoya suke jefa kansu ciki wadda har ta kai ga wasu sun yi aure amma zaman auren ya ci tira.
Yana da kyau masoya su sani yayin da masoyinsu ya sanar da su cewa yana son su alhalin su ba sa sonsa toh su sanar da shi cewa ya yi hakuri an riga an yi wa wani alkawari, tare da lallamar cewa “Shi aure nufi ne na Allah in Allah ya nufa kai ne mijina ba tsumi babu dabara amma yanzu ka yi hakuri ka ga ba dadi an riga an yi alkawari da wani”
Haka ma idan namiji ne ya tsinci kansa cikin hakan wata na sonsa ba ya so sai ya sanar da ita badan komai ba sai dan zuciyarta ta samu kwanciyar hankali koda kuwa ta ji damuwar rashinsa.
Sabanin kai tsaye a sanar wa mutum cewa “Ni ba na sonki/ba na sonka, wannan kalmar ta rashin so da ake fadarta kai tsaye ba karamar matsala ba ce masoya, saboda wasu ta wannan kalmar suke neman cutar da wanda suke so muddin ba sa sonsa, kuma na tabbata duk wanda aka furtawa ita ba zai ji dadi ba, don haka fadarta kai tsaye yana da matukar matsala.
Sai dai kuma wasu a kan sanar da su din ta hanyoyin da suka kamata amma sai su kafe su ce su lallai tunda ba daura aure a kai ba ba su ga dalilin da zai sa su janye kudurinsu kan wanda suke so ba koda kuwa mace ce take son namiji duk wulakancin da zai mata tsaf! Zata shanye ba za ta ji komai ba.
Kafewa kan hakan yana kawo wulakanci ga wanda kake so shi kuma ba ya sonka, babu dadi ko kankani a wulakanta masoyi yana da kyau kowanne bangare su yi kokarin gyarawa don samun masalaha ga juna da kuma zama cikin kwanciyar hankali.
Toh! Nawa aka yi? Ai akwai masoya da dama wadanda har su yi aure da wasu daban amma zumuncin su be ruguje ba ana ganin juna a mutunce, ina nufin wadanda suke kai kokon barar soyayyarsu ba su samu abin da suke so ba, amma dalilin bayani cikin lumana sai zancen so ya wuce a runka kawai gaisawa har Allah ya sa kowanne ya auri wanda yake son aura, wanda wasu ba haka yake a wajensu ba yayin da suka ce suna son mace ita kuma taki amaincewa sai a dauki karan tsana a dora mata, haka ma idan macen ce take son namiji ya ki amincewa sai ta dauki karan tsana ta saka masa don kawai ya ce yana da wadda yake so ko kuma dan ta sanar da shi akwai wanda ya riga shi.
Abin tambayar a nan shi ne, ina wannan son da ake wa macen ko kuma ake wa namijin? Ko daman ba son gaskiya ba ne so ne don wani manufa na daban?
Yana da kyau masoya su gyara zamantakewar soyayya da kuma al’amuran da suka shafi soyayya gaba daya don zaman masoya lafiya da juna.
Na ji ta bakin daya daga cikin masoya.
Sulaiman Uthman Khalid daya ne daga cikin masoya a tattaunawarsa da muhiebert India ya yi bayani kan wata matsala wadda ta fi bata masa rai ta masoya ga abin da yake cewa:
Ba abin da ya fi batan rai a soyayyar tsakanin saurayi da budurwa irin na ga saurayi yana da ‘yan mata ba adadi, ya je gun waccan ya je gun wannan, kuma don wulakanci duk sai ya yi alkawarin zai aure su, amma abin bakin ciki cikinsa ma da kyar yake iya ciyar da kansa, sai karya fal ciki, wannan abu yana batan rai sosai.
A wannan lokaci a duk sanda mace ta fito hira da wani namiji in har macen kirki ce ba ta da wani bukata da ya wuce ta ga ta auri wannan saurayi da suke tare, amma mu samari na wannan lokaci da yawanmu wallahi mun riga mun lalace, yaudara da karya da fafa ita ce abin da samari suka sa gaba, an ya kuwa za a kwana lafiya? Allah ya sa mu dace.
Ya za ka kwatantawa masoya yanda yaudara take? Kuma taya ake gane saurayi mayaudari?
Yaudara sigoginta da fannoninta suna da mutukar yawa a soyayya , kuma ita ce babbar cuta abar cutarwa ga wanda ko da wacca aka yaudara, yaudara ita ce silar rugujewar komi na soyayya, yaudara tana ja wa mutum ya zautu ko ma ya rasa ransa gaba daya saboda tsananin ciwonta ga wanda aka yaudara.
Masana da kuma masu sharhi sun ce ana gane saurayi dan yaudara wajen kalaminsa, saurayi dan yaudara ya iya kalami na soyayya mai sace duciyar budurwa nan take, domin har karanta suke, don mun san irinsu, kuma za ku gansu da son fafa da son a san su wasu ne, ako ina ba sa boye kansu kawai don a ce su ‘yan birni ne, suna so su yi abin da za su birge budurwa, za su iya kashe ko nawane don cim ma wata manufa ta su, shigarsu ma ta musamman ce, wasu matan kuwa suna mutukar son irin su ba su san babbar annoba ba ce a gare su.
Wacce Matsala kake ganin masoya za su gyara a soyayyarsu?
A gaskiya matsalar da ya kamata masoya su gyara a soyayyar su shi ne, a yi soyayya tsakani ga Allah a cire yaudara a ciki, kuma ka da mutum ya ce zai yi soyayyar karya, kai ba don kowa ba ka ce kai dan wani ne kawai don ka ja ra’ayin mace ta soka, wannan ba yi ba ne, sannan suma matan su cire kwadayin abin duniya, in kuwa kika sa abin duniya a gabanki hakan zai sa ki ta haduwa da samarin karya da na banza har wani ya zo ya yi silar rugujewar cikakkiyar rayuwarki. Mata ku dinga lura da sanin wane saurayi ya dace ki kula ki yi bincike a bisa cikakkiyar halayyarsa, kamar yadda sauran samari na gari suke bincike a kan halayyar matan idan sun zo neman auren su, Allah ya sa mu dace.
Amin, sulaiman da fatan masoya za ku yi amfani da shawarar da Sulaiman ya bayar don samun ingantacciyar soyaya, kadan ke nan daga tattaunawar da muka yi, ku tara wani makon don jin da me zan zo muku.