Na dade Ina nazari a kan matsalolinda matasa ke fuskanta a siyasa. Mafi Yawan Matasa Su Na Da Ra’ayin Siyasa, Sai Dai Kuma Ƴan Siyasa Sun Mallake Su, Sun Tsuke Matasa A Wuri Guda Ba Tare Da Sakar Musu Cikakkiyar Damar Da Za Su Dama Domin Gobensu Ta Yi Kyau Ba.
Yau Juma’a, 27 Ga Watan Maris ta Shekarar 2020.
Matasa ba su da baƙin zaren yin nazarin abubuwa da fidda tsaki cikin tsakuwa. Mu na yin amfani da rayuwarmu akan nazarin abubuwa da ɗabi’unmu kan tambaya daga iyayenmu da malamanmu da masu ba da aiki da abokanmu. Mu na rayuwa tare da ƴan siyasa da ƴan jarida waɗanda za su nemi ƙalubalantar ɗabi’unmu.
Ra’ayoyinmu sun zamto ana sauraronsu amma shugabanni daga cikin al’umma ba sa ɗaukansu da muhimmanci. Mafi yawan matasa su na da ra’ayi da ya shafi matakan zartar da hukunci da ke taɓa rayuwarmu ta yau da kullum. Dukkanmu mu na maida hankali ne akan rayuwarmu tagaba inda mu ke tafiyar rayuwa a tsakanin wariya da ake nuna mana da kuma rashin ba mu damar samun ilimi da kiwon lafiya da aikin yi da kuma samun damar mallakar muhalli cikin sauƙi.
Aikina na jarida dakuma rubuce-rubucena a yanar gizo, ya taimaka min ƙwarai wajen ƙara buɗewar idanuwana da fahimtar yadda al’amura su ke tafiya da kuma matsaloli da ƙalubalen da matasa su ke fuskanta. Mafi yawan matasa ƴan gwagwarmaya a cikin al’umma kaɗan ne su ke samun cikakkiyar dama daga ƴan siyasa da ma kafafen watsa labarai wajen jin ra’ayoyinsu da karɓar shawarwarinsu da kuma ba su damar tafiyar da tsare-tsare da ayyukan al’umma.
Ya zama wajibi a ba wa matasa damar da za a tattauna harkokin siyasa da mulki da su. Sannan kuma a ɗauki muhimman shawarwarinsu kan tsare-tsare da za a aiwatar. Domin matasa masu tasowa musamman ƴan shekaru 16 zuwa 21 da 25 zuwa sama, rukunin matasa, su na da basira da tunani mai kyau wanda zai taimaka in da za ayi amfani da shi. Sannan kuma a ɗauki bayanai kamar na yawan kuɗin makaranta da su ke biya da kuma ƙarancin walwala a sakar musu dama su samu kykkyawar rayuwa.
Ya zama wajibi siyasa da gidajen jaridu su manta da bambance-bambancensu, su haɗa kai tare domin shigar da matasa tare da ɗaukar ɗawainiyar kula da rayuwarsu tagaba. Ilimi da samar da walwala ga matasa nauyi ne da ya rataya akan dattijai su ba wa matasa. Su ƙarfafe mu wajen damawa da mu a cikin tattaunawa. Ya zama wajibi ƴan siyasa da ƴan jarida su riƙa maida hankali wajen tattauna batutuwa masu alaƙa da matasa sannan kuma su sanya su a hanyar da za su gane al’amura da wannan dalili ne yasa nayi sha’awar bude wannan Shafa na “zauren matasa” a jaridar nan mai farinjini wato leadership Ayau.
Shugabanninmu ba su mance da sanannun al’adu a tsakanin matasa ba, hakan zai zama abu mai sauƙi su ɗauki fitattu daga cikinsu su bayyana ra’ayoyinsu. Matasa su na buƙatar shugabanni da ƴan jarida su ba su dama wajen gabatar da ra’ayoyinsu da tunaninsu da kuma bayyana matsaloli da damuwarsu. Wannan juyin juya hali ne wanda zai kawo gyara kan halin da matasa su ke ciki dangane da damar da ake hana su.
Matasa su na da ƙorafin neman su ba da gudunmawa kan muhawarorin siyasa da dama, sai dai a mafi yawan lokuta ba a cika ba su wannan damar ba. Ya zama wajibi a tashi tsaye, a cigaba da damawa da matasa domin ganin sun samu murya da damar ba da gudunmawarsu cikin tattaunawar siyasa da tafiyar da harkokin mulki da jagorancin jama’a. An bar matasa kamar kara a zube, komai ƴan siyasa masu tarin shekaru ne su ke tafiyar da shi, an tauyewa masa damammaki da haƙƙoƙinsu.
Dukkan wasu harkoki da damammakin siyasa su na jujjuyawa ne a tsakanin tsofi su ne su ka mamaye komai da kowa an bar matasa a gefe ɗaya. Matasa ake bari da kaɗa ƙuri’a da wahalhalun siyasa. Kuma su ake bari da shan wahalar samun aiki da haƙƙoƙinsu da za su taimaki gina rayuwarsu. Lokaci ya yi da ya kamata tsaffi janyo masa su ba su dama a dama da su domin su ma su samu kykkyawar rayuwa mai inganci. Ɗumbin matasa su na son a saurari shawarwarinsu a kuma ji matsaloi da damuwarsu, amma an hana su wannan dama. Ƴan kaɗan daga cikin matasan waɗanda su ke iya samun damar bayyana ra’ayinsu a mafiyawan lokuta su ma ba a yin amfani da shawarwarin nasu, balle a magance musu matsalolinsu ko a ba su haƙƙoƙinsu. Idan ya kasance tsaffin ƴan siyasa sun ba wa matasa kulawa da dama to ba shakka matasa za su samu cigaba mai girma. Ni Rukayyat Sadauki Ina kara kira fa matasa a kan mu kara himma wajen ganin mun yi amfani a wajen da ya kamata kuma an dama da mu.
Na gode!