Matsalolin Sabon Gari Za Su Kau In Har … – Musa Ahmed

Sabon Gari

A kwanakin baya ne jam’iyyar APC a karamar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna, ta tsayar da fitaccen dan siyasar nan da ake kira ALHAJI MUSA AHMED MUSA, wanda aka fi sani da MUSA A. MUSA a matsayin wanda zai tsaya wa jam’iyyar takarar cike gurbi na majalisar Kaduna a mazabar Sabon gari, wanda zai gudana nan ba da jimawa ba. Wakilinmu da ke Zariya ISA ABDULLAHI GIDAN BAKKO, ya sami damar tattaunawa da Alhaji Musa A. Musa kan abubuwa da dama da suka shafi takararsa da matsayin jam’iyyar APC a karamar hukumar Sabon gari da kuma sauran batutuwa da dama.

Ga yadda tattaunawarsu ta kasance,

 

Ya ka dubi wannan dama da jam’iyyar APC da kuma magoya bayan jam’iyyar suka ba ka na yin takara zuwa majalisar jihar Kaduna a zaben cike gurbi da zai gudana a ranar 19 ga watan Yunin wannan shekara ta 2021 ?

 

A gaskiya da farko baa bin d azan ce sai godiya ga jam’iyyarmu ta APC da ta b a ni wannan dama, kuma su kan su ‘ya’yan jam’iyyar da iyayen jam’iyyarmu dole in gode ma sun a ba ni wannan dama ta in wakilce su a majalisar jihar Kaduna a zaben cike gurbi a nan mazabar Sabon gari, kuma ‘ya’yan jam’iyyar APC sun yi haka ne domin sanin irin gwagwarmayar da mu ka dade mu na yi a wannan karamar hukuma ta Sabon gari, suka yi karatun baya na gudunmuwar da na ke bayarwa a duk wata harka na al’umma da kuma siyasa, to lallai, ina kara godiya.

 

Wani salon wakilci al’ummar mazabar Sabon gari za su gani daga wajen ka, da zarar ka sami zuwa majalisar jihar Kaduna ?

 

Abin da zan shaida wa al’ummar mazabar Sabon gari da kuma karamar hukumar Sabon gari baki daya, duk wanda ya sanni, ya sanni a matsayin mutum da rungumar hidimar al’umma dare da rana, to in Allah ya sa mun sami nasarar wannan zabe, abubuwanda za mu ci gaba da su ke nan, da yadda wanda ya halicce mu.

Duk wannan mazaba da na ke yin takara da kuma karamar hukumar Sabon gari, duk dai – dai gwargwado, na san matsalolin da suke addabar al’ummomin da suke wadannan wurare, in Allah ya yadda, abin da gwamnati ya kamata ta yi, za mu tsaya mu ga gwamnati ta yi wadannan abubuwa, in kuma wadanda mu ne za mu yi, in sha Allah, za mu yi bakin iyawarmu, inda mu ka kasa kuma, mu na addu’ar Allah ya kara ba mu damar yin su a lokutan da suka dace.

 

Wani tabbaci za ka ba al’ummar mazabar Sabon gari na yadda mafiya yawan ‘yan siyasa tamkar hawainiya su ke, na a kwai yiwuwar kila a sami canji ?

To babu abin da zan ce a nan sai dai in ce duk wanda ya sanni, ya san wanene ni daga 1999 zuwa yau na rungumar hidimomin jama’a a nan  karamar hukumar Sabon gari, amma wadanda ba su sanni ba ne za su yi tunanin ganin wani canji daga wakilcin da zan yi.

Kuma duk wani dan siyasa da ke nan karamar hukumar Sabon gari, in dai a tafiyarmu ne, mun san ko shi wanene, kuma mun san kan mu har zuwa yau.Wadannan matsaloli ne suka sa al’umma suka ce su na son canjin wanda zai wakilce ya san matsalolinsu, ya kuma saba warware ma su matsalolinsu da karfinsa da karfensa dare ko rana, adu’a ta ita ce, Allah ya ba ni ikon aiwatar da abubuwanda al’umma ke bukata na wakilcin d azan yi ma su a majalisar jihar Kaduna, abin da dai na ke bukata shi ne al’umma su ci gaba da yi ma na addu’o’in da za su zama silar fuskantar ayyukan da za a dora ma na ta yadda za mu sami nasarar duk abin da mu ka sa wa gaba da suka shafi al’ummar mazabar Sabon gari da kuma karamar hukumar Sabon gari baki daya.

 

Mata a siyasa na yawan kukar a na mayar da su tamkar gugar – yasa, wani canji mata za su gani a wakilcin da za ka yi in mai duka ya yadda da mata za su iya cewar kakarsu ta yanke saka ?

 

To, mu dai a batun siyasa a karamar hukumar Sabon gari, musamman a jam’iyyar APC, mun san halin da mata ke ciki, mun san abin da ake yi ma su, kuma da yaddar mai duka, mata za su kara amfana da dukkanin abubuwanda suka dace, ba lallai sun motsa ba, in dai hakkinsu ne, zai gangaro har inda suke, kamar yadda aka saba yi ma su a duk tafiyar siyasar da mu ke yi a karamar hukumar Sabon gari.

Zan bayar da misali da tallafin da dan majalisar wakilai ke bayarwa, wato Alhaji Garba Datti Babawo, mata da suke kungiyoyi su na amfana da kuma dai – daikun mata a nan karamar hukumar Sabon gari, duk a na tallafa ma su, matan sun san haka, sai dai kuma za mu kara zage damtse, domin tallafa wa mata a duk bangarorin da suka dace.

 

 Ya ka dubi karbuwar jam’iyyarku ta APC, musamman a matsayin ka na dan takara ?

Babu ko shakka, jam’iyyar APC na nan da karsashin ta da kuma farin jinin ta, musamman in ka dubi yadda al’umma suka fito suka sabunta rijistar jam’iyyar, a nan za ka fahimci jam’iyyar APC a nan fiye da yadda ta ke a farkon kafa ta, kuma ka sa ido, ba karamar hukumar Sabon gari ba, jihar Kaduna ta jam’iyyar APC ne.

 

 

Exit mobile version