A yau galibin mutanen da suke zaune a cikin wannan kasar tamu suna cikin wani irin yanayi na tsoro saboda rashin tsaro da kuma rashin cigaba . In aka yi la’akari da irin yadda Allah ya albarkaci Kasar da dumbin arziki da kuma yawan al’umma musamman matasa masu jini a jika sun kai akalla kashi 70% sai in ce babu wani shiri da hukumomi suke yi musamman a matakin jiha da kananan hukumomi da zai inganta rayuwar wadannan al’umma tamu.
Wadannan hukumomi (jiha da kananan hukumomi) mutane basu cika damuwa da bibiyar aiyukan su ba duk da sune mafi kusa da su.kafin ka ji wani ya ambaci sunan shugaban karamar hukumar sau daya ya ambaci sunan shugaban kasa sau dari. Hasalima da yawa ko sunan su ba su sani ba.
Mutane sun fi maida hankalisu a kan meye gwamnatin tarayya ta yi, me ye ba ta yi ba alhali ga gwamnatoci kusa dasu amma basu damu damai suke yi ba.duk da suma ana basu nasu kason daga kasafin da ake bayarwa na dukiyar kasa saboda haka ya zama dole akan su suyi ma mutanen su aiki. ya kuma zama dole a kan mutane su binciki yanda ake kashe wadannan kudaden da ake bayarwa dominsu musamman, a matakin kananan hukomomi.
Babban muhimmin abunda yake kan gwamnati a ko ina a fadin duniya shi ne samar da ababen more rayuwa ga talakawa. Tun lokacin da Nijeriya ta samu yancin kai a shekarar 1960, hukumomi sun fitar da tsaren tsaren yanda za’a inganta rayuwar talaka.
Babban abunda sukafi maida hankali akai wajen tsare tsaren nasu da kudurorin su shine yankunan karkara duba ga mafi yawancin mutane suna zaune ne a wannan yankin.samar kananan hukomomi ga mutane ya samo asali ne ta haka domin kuwa shine gwamnatin dake kusa da mutane.
Babban muhimmin dalilin da ya sa aka kirkiri kananan hukumomi shi ne, domin a kawo gwamnati kusa da mutane don inganta yanayin rayuwarsu. Saboda haka, yanzu a Nijeriya muna da matakin gwamnatoci guda uku, tarayya, jiha da kuma kananan hukumomi, kuma kowacce daga cikin su tana cin gashin kanta na yadda za ta gudanar da aikace aikace ga mutane a hukumance.
Kananan hukumomi su aka ba mawa alhakin kula da ilimi a matakin firamare, kula da hanyoyi da gadoji da kuma kula da kasuwanni. Babban muhimmin abun da da kananan hukumomi za su samar wa mutanen su shi ne Ilimi, tsabtaceccen ruwan sha da kuma kananan asibitoci daga harajin da suke samu, hakan zai tabbatar da cigaba ba na mutanen karkara kadai ba har da kasa baki daya.
Sanin kowa ne muna cikin wani mawuyacin hali na rashin tsaro a yankin nan namu na arewa.garkuwa da mutane don kudin fansa, kisan gilla na yan bindiga ya zama ruwan dare. Ko a satin da yawuce sai da aka yi garkuwa da Manyan ‘Yan Sanda 12 masu matsayin ASP da aka tura su aiki na musamman daga Jihar Borno zuwa Katsina da Zamfara. In dai har za a yi garkuwa da wadanda aikinsu shi ne kare rai da dukiyoyi, to waya tsira? Irin wannan ta'addacin na Boko Haram da na tsagerun
yan bindiga yana nema ya zama jiki ta yadda ba za ka ga ana buga shi a matsayin labari mai daukar hankali ba.
Yanayin yanda abun yake faruwa kusan koda yaushe, hakan bai cika daukar hankalin hukumomi ba, wajen yin habbasa naganin an magance shi, akwai yiyuwar kasar za ta kasance tamkar wadda ba gwamnati domin kuwa babu doka da oda a halinda a ciki yanzu. Duk inda ya zama mutane za su ci Karen su ba babbaka to lallai babu kyakkyawan jagoranci daga hukomomi.
Duba ga muhimmanci zaman lafiya wurin kawo cigaban mutane da karuwar arziki da walwala ya zama dole kananan hukumomi su shiga a dama dasu wajen taimakawa jami’an tsaro ta hanyar gina kyakkyawan alaka tsakaninsu da mutane hakan zai taimaka wajen samun bayanai masu muhimmanci daga wurin jama’a ta yadda za a magance matsalar tsaro, sannan kuma su taimakawa wajen sama musu tallafi na kayan aiki.
Domin kuwa har sai kansiloli da shugabanin kananan hukomomi sun san cewa yanada daga cikin nauyin daya rataya a kansu, su tabbatar da cewa duk wanda yake zaune a gundumominsu sun kare masa dukiyar sa da rayuwar sa sannan za a samu dawamammen zaman lafiya mai dorewa.
Su kuma mutane sai sun san cewa har sai sun taimaka wajen bayarda ingantattun bayanai ga jami’an tsaro da hukomomi sannan za’a samu damar magance wannan gagarumar matsala ta rashin tsaro da yaki ci yaki cinyewa a yankin mu mai albarka.
Daga karshe matsala ta harkan tsaro da kuma kawo cigaban kasa baya tsaya akan hukomomi bane kawai, abune da ya shafi kowa.duk wani dan kasa mai kishi da yasan abunda yake yana da rawar da zai taka wajen ganin an magance matsololin da suka addabe bu. Allah yamana gudunmawa. Amin.