Matsayin Kirista A Duniya Tamkar Gishiri Ne A Abinci (II)

Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru 0806 871 8181 yyohanna@gmail.com

Gaisuwar ban-girma ga masu karatun LEADERSHIP A YAU. Da fatan kuna nan lafiya, da fatan zaman lafiya a ƙasarmu ta gado, wato Nijeriya. Godiyarmu Kiristoci na zarafin da aka ba mu domin Bishirar addinin Kirista a wannan Jirida mai albarka. Mun gode Allah ya saka da Alherinsa, Amin.

Karatunmu na samuwa daga littafin Matta 5:13-16. Za mu ci gaba daga wurin da muka tsaya a makon da ta gabata. Matta 5:14 Yesu ya ci gaba koyarwa cewa: “Ku ne hasken duniya. Birnin da ke kafe bisa tudu ba shi ɓoyuwa.”

Yesu daga aya 13 ya kira Almajiransa “Gishirin Duniya.” Baicin haka, ya kuma tabbatar masu da cewa irin kyawawan halaye ne kaɗai zai iya bambantasu da kowane irin mutane. Su ne za su zama sanadin zaman lafiya a duniya, ta wurin haɗa kan jama’a, su ne za su sa duniya ta yi daɗin zama ga kowa da kowa. Kuma Kiristoci su ne sinadarin tsarkake al’umma ko duniya daga abubuwan da ba su da kyawu domin ta yi kyawu da samun salaman zaman lafiya.

Yesu yana tabbatar wa Almajiransa da cewa, in ko su Almajiransa ko Kiristoci ba su cika waɗanan abubuwan nan gudu huɗu, gishiri na yi a cikin abinci ba, ko ya kamata Kirista ya yi rayuwa mai kyau ko ingantacciyar rayuwa yadda gishiri yake a cikin abinci domin duniya ta sami zaman lafiya. To Kirista ba shi da wata kima ko daraja ko ingantacciyar rayuwar da zai bambata shi a duniya, wato Kirista ba shi da ko amfani kuma, kyawunshi a zubar da shi a kuma tattaka shi.

A nan ne za mu ɗora akan jawabinmu. Yesu ya tabbatar da cewa: “Ku ne hasken duniya. Birnin da ke kafe bisa tudu ba shi ɓoyuwa” (Matta 5:14).

Wannan ayar mun gano wata suna ne. kuma da Yesu Almasihu ya baiwa Almajiransa ko Kiristocin duniya gaba ɗaya. Amma a Littafin Yohanna 9:5 Yesu ya nuna wa Almajiransa ko Kiristoci da cewa matuƙa shi yana nan duniya, to babu wani haske baicin shi ne hasken duniya.

Amma ga yadda shi Yesu ya tabbatar mana da cewa: “Sa’anan ina cikin duniya, ni ne hasken duniya” (Yohanna 9:5).

Wato a nan Yesu shi ne hasken duniya in dai yana nan duniya, amma matuƙar ya yi ƙaura da duniya, to su Almajiransa ko Kiristoci sun zama wakilansa a matsayin fitilar duniya domin su haskaka a duniya. Wato, Kiristoci sun zama magadan hasken da ke wurinsa da duniya ke buƙata.

In Yesu shi ne hasken duniya, amma sai ya koma ya kirawo Almajiransa ko Kiristoci cewa su ne kasken duniya, to ma’anan shi ne su Almajiransa ko Kiristoci sun zama wakilansa masu kyawawan halaye da za su yi wata rayuwa mai kyau da mutanen duniya za su shaida.

A cikin Littafin Yohanna, Yesu ya ci gaba da cewa: “Yesu fa ya koma yi masu magana, ya ce, Ni ne hasken duniya: wanda ya biyoni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.” (Yohanna 8:12).

A nan Yesu ya ƙara tabbatar wa Almajiransa ko Kiristoci da cewa babu wani mutum da ya isa ya zama hasken duniya baicin shi kaɗai. Amma Yesu da kansa ya kira Almajiransa ko Kiristoci da cewa su ne hasken duniya ko fitilar duniya.

A wannan ayar, Yesu ya ce duk wanda ya biyo shi ba zai kasance cikin duhu ko dufu ba. Wato rayuwar Kiristoci ko Almajiransa kamar hasken fitila, wanda duniya za su shaida hasken su kamar yadda fitila ke da haske duniya na gani.

Duka wannan koyarwar da Yesu na yi akan fitilar duniya ko hasken duniya, yana ƙoƙari ya nuna wa Almajiransa ko Kiristoci matsayinsu a duniya a matsayinsu na Mabiyansa. Yesu na so kowane mutum da ya yi imani gare shi, ya San da matsayinsa a duniya da cewa ya zama dabam, domin shi Krista ne.

In mun koma ga Matta 5:14a: “Ku ne hasken duniya:” A Yohanna 9:5 da Yohanna 8:12 mun gane da cewa waɗanan ayoyin sun tabbatar da cewa Yesu karankansa shi ne haske duniya. Amma ya kira Almajiransa ko Kiristoci da cewa su ne hasken duniya ko fitilar duniya. A nan Yesu yana tabbatar mana waliyyanci ko wakilci.

Almajiransa ko Kiristoci masu imani da Yesu Almasihu, su ne hasken duniya. Domin suna cikin Yesu, rayuwarsu ta zama kamar ta Yesu. Irin hasken da ke cikin Yesu na cikin Almajiransa domin na cikinsu.

ɓ14a: “Ku ne hasken duniya,” alama ce cewa matuƙar Kiristoci suna duniya, to su ne hasken duniya. Domin kyawawan halayen Kiristoci, haske ne ga duniya gaba ɗaya.

ɓ14b: “Birnin da ke kafe bisa tudu ba shi biyuwa.” Da Yesu ke wa Almajiransa wannan maganar, yana sane da cewa sun san da biranen Judea da Bethlehem an gina su akan tudu ne ko akan duwatsu ne.

Yadda gine-ginensu na kan tudu ba su ɓoyuwa, to haka ne kyawawan halayen cikaken Kirista da ba su ɓoyuwa. Yadda gini a bayane ba a ɓoye yake akan tudu ba, to haka ma halayen Kirista a ko’inna yake ba ya ɓoyuwa.

Da shike halayen Kirista da rayuwarsa ba sa ɓoyuwa, kamar ginin da ke kan tudu. To shi ya sa Yesu yana gaya wa Almajiransa ko Kiristoci da cewa, ko ina ku keKu dabam kuke. Kuma duniya na kallonku. Shi ya sa ko da dan abu kaɗan ne in dai da hannun Kirista ne, to dai ta bayyana.

A nan Yesu na nuna wa Almajiransa ko Kiristoci da cewa matuƙar ku Almajiransa ne ko Kiristoci ne na gaskiya, to babu yadda halayen za su ɓoyu domin rayuwar Kirista na nan a bayyane, kamar birnin da aka gina akan dutse da kowa na gani a bayyane.

Duk Kirista na gaskiya shaida ne na Yesu Almasihu. Ayyukan Manzanni 1:8 ya tabbatar man’s wannan gaskiyar da kuma Littafin Ibraniyawa 12:1. Akwai kuma shaidun da ke kewaye da mu. To Ashe kowanne irin hali ne muke da shi, mai kyau ko mara kyau, babu yadda za mu iya ɓoye su domin a bayyane suke ga duniya. Kuma duk mutanen duniya suna kallonmu dare da rana.

A ƙarshe, kowanne cikakken Kirista shi kama dutsen Urushalima ne, Littafin Ishaya 2:2. Ma’anar, ita ce kowa na kallon Kirista a matsayin misali ga kowa da kowa.

 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa daga nan. Shalom! Shalom!! Shalom!!!

 

Exit mobile version