Tuni wasu rahotanni daga kasar Ingila suka fara bayyana cewa korar da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta yiwa kociyan kungiyar Thomas Tuchel zata iya hana dan wasa Kylian Mbappe komawa Real Madrid a karshen kakar wasa.
A ranar Alhamis din data gabata ne kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kori Thomas Tuchel, dan asalin kasar Jamus sanarwar da akasarin kafafen yada labaran Faransa dana nahiyar turai suka yi ta yadawa ta tabbata.
Thomas Tuchel na daga cikin mutanen da suka taimakawa kungiyar ta PSG tsawon lokacin da ya share da babbar kungiyar PSG kuma ya lashe kofuna da dama a kungiyar tun bayan komawarsa daga kungiyar Borussia Dortmund ta kasar Jamus.
Rashin lashe kofin zakarun Turai ya sa magabatan kungiyar ta PSG suka yanke shawarar korar Tuchel bugu da kari a wannan kakar wasan kungiyar bata buga abin arziki a gasar lig one ta kasar Faransa kuma tuni kungiyar ta shiga tattaunawa da wani makusancin Tuchel, dan kasar Argentina Mauricio Pochettino.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tayi alkawarin sayan dan wasa Mbappe idan an kammala kakar wasan bana wanda hakan ne yasa kungiyar bat sayi dan wasa ko daya ba a kasuwar data gabata saboda tana tara kudin sayan Mbappe.
A kwanakin baya dan wasan shima ya bayyana cewa bashi da burin ci gaba da zaman kungiyar kuma yana fatan a karshen kakar wasa zai koma daya daga cikin kungiyoyi manya a nahiyar turai.
Shi ma dan wasa Neymar, wanda baiji dadin korar da akayiwa Tuchel ba, yana bukatar tsayawa domin karatun ta nutsu akan yanayin da kungiyar zata kasance nan gaba duba da har yanzu ba’a san wanda kungiyar zata dauka ba.
A kwanakin baya Neymar ya bayyana cewa zai iya barin kungiyar ta PSG idan har shugabannin kungiyar ba suyi kokarin sayo dan wasa Messi ba wanda yake shirin barin Barcelona a karshen kakar wasa ta bana.
Sai dai PSG za ta fuskanci kalubale daga wajen wasu daga cikin manyan kungiyoyi kamar Manchester City, wadda kociyan kungiyar yake da alaka mai kyau da Messi sai kuma kungiyoyin Chelsea da Inter Milan.