Daga Khalid Idris Doya
Wata uwa ‘yar shekara 21 a duniya, Emila Sunday, an cafketa bisa zargin yunkurin saida jaririnta dan watanni uku a duniya a Ojoto da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu da ke jihar.
Wacce ake zargin ‘yar asalin jihar Akwa Ibom ce, an bada rahoton cewa ta yi yunkurin saida karamin yaronta a kan kudi naira N150,000.
Ta nuna cewa ta aikata hakan ne bisa tsananin talauci da fatara da ta fada.
Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin ‘yan sandan jihar Haruna Muhammad, ya shaida cewar an kame wanda ake zargin ne da yammacin ranar Talata a yanki.
Ya ce: “A ranar Talata da karfe shida na yammaci, biyo bayan samun rahotonnin sirri, jami’an ‘yan sanda da ke aiki a karkashin caji ofis din Ojoto da ke Anambra, sun cafke wata mata mai suna Emila Sunday wacce ta yi ikirarin cewa ita ‘yar jihar Akwa Ibom ce mai shekarun haihuwa 21 a duniya, da danta ‘yar wata uku a kauyen Ire Ojoto.
“Binciken farko-farko ya nuna cewa matar ta yi kokarin saida danta, dan wata uku da ta yi ikirarin cewa matsatsin rayuwa ne ya sanyata hakan.”
Haruna Muhammad ya shaida cewar an samu nasarar ceto yaron cikin kwashin lafiya, yana mai karawa da cewa bincikensu na cigaba da gudana domin gano yadda lamarin ya ke.