Mauludi: A Yi Koyi Da Dabi’un Manzon Allah Don Gina Al’umma Ta Gari

Tallafin

Daga Khalid Idris Doya

Yayin da Musulmai a Jihar Gombe suka bi sahun takwarorinsu na sassan duniya kan murnar zagayowar bikin Maulidi na bana wanda ya fara gudana tun daga ranar Alhamis, inda jama’an jihar suka himmatu wajen nuna murnarsu da wannan babbar rana ta zagayowar ranar haihuwar fiyayyen Hallita.

Cikin annashuwa da kwanciyar hankali jama’a suka fara bukukuwan Maulidi a jihar ta Gombe, inda aka samu cigaba matuka ta fuskacin tsari da nagartar bukukuwan a bana.

A sakonsa na wannan shekarar, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya mika sakonsa na taya murna ga al’ummar Musulmin jihar, yana mai kira a garesu da su rungumi dabi’un hakuri, kankan da kai, tawali’u da kyautatawa kamar yadda Manzon Tsira Annabi Muhammad S.A.W. ya koyar a yayin rayuwarsa.

Gwamnan ya kuma bukaci shugabanni da mabiya su yi amfani da damar bikin wajen daukan darusa daga halaye da dabi’un ma’aikin Allah Muhamamd dan Abdullah na yawan hidima da son zaman lafiya tsakanin al’umma, da bada tasu gudunmowa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al’umma.

Ya kuma yi bukatar ci gaba da addu’o’in zaman lafiya, walwala da ci gaban Jihar Gombe da Nijeriya baki daya.

Gwamna Inuwa ya kuma jaddada bukatar ci gaba da hakuri da juna tsakanin mabanbantan al’ummar jihar ba tare da la’akari da banbancin dake tsakaninsu ba, yana mai kira a gare su su ci gaba da bin doka da oda, su kuma yi dukkannin mai yiwuwa na ganin sun kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin da Jihar Gombe ke da shi, ta hanyar kauracewa duk wani abinda ka iya gurgunta zaman lafiyan jihar.

Ana dai cigaba da bukukuwar ranar Maulidi a jihar Gombe cikin kwanciyar hankali ba tare da wani matsala ba.

Exit mobile version