Sulaiman Ibrahim" />

Mauludi: Gwamnonin Arewa Sun Yi Kira Da Hakuri Da Soyayya Ga Juna

Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi kira da a yi hakuri da nuna kauna a tsakanin ‘yan Najeriya da sauran Musulmin duniya don farin ciki a kan bikin Mauludi.

Gwamna Simon Lalong na Filato kuma Shugaban kungiyar sun yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa daga Daraktan sa na yada labarai da hulda da jama’a, Dakta Makut Macham, a ranar Alhamis a Jos.

Ya ce ya kamata dukkan musulmi su yi amfani da wannan dama wajen yin tunani a kan kyawawan dabi’u na kauna, hakuri da juna kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya nuna.

A cewarsa, halin da kasar nan ke ciki a yanzu na bukatar yin tunani mai kyau da kuma bukatar hakuri, fahimta, gaskiya, kirki da hadin kai wajen shawo kan kalubale iri daban-daban na kasar.

Shugaban ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi addu’a domin karin hikima da shiriya wajen baiwa shugabanni damar yi wa mutane hidima ta hanyar shirye-shirye da manufofi wadanda za su magance talauci da inganta jin dadin su.

Lalong ya kuma yi kira da a kwantar da hankula biyo bayan abubuwan da suka faru kwanan nan yana mai tabbatar da cewa gwamnati na daukar duk matakan da suka dace don magance matsalolin da matasan Nijeriya suka gabatar.

Ya yi kira ga matasa da su guji fitinar lalata dukiya wanda, a cewarsa, aikata hakan bai jawo komai sai hana ci gaba.

Exit mobile version