Mawakiya Rihanna Ta Ja Hankalin Duniya Kan Ilimi

Shahararriyar mawakiyar nan ta Amurka Rihanna ta bukaci jama’a da kada su karaya a yunkurin bunkasa ilimi har sai dukkanin yara sun samu karatu a fadin duniya.

Rihanna ta fadi haka ne lokacin da ta bayyana tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron a wurin taron gidauniyar bunkasa lilimi a Dakar na kasar Senegal.

Haka nan kuma mawakiyar ta yi kira ga shugabannin kasashen yammacin duniya da firaministan Burtaniya Theresa May su tallafa wa gidauniyar.

Shugaba Macron na Farnsa ya bayyana ilimi a matsayin makamin yaki da ra’ayin rikau da rikice-rikicen da ke addabar yammacin nahiyar Afirka.

Ya kuma yi alkawari bayar da Yuro miliyan 200 a matsayin tallafi ga gidauniyar da ta shirya taron.

 

Exit mobile version