Bello Hamza" />

May Ta Sake Shan Kaye A Majalisa Kan Yarjejeniyar Brexit

Firaministar Birtaniya Theresa May ta sake shan kaye a gaban Majalisar kasar, inda ‘yan Majalisu 391 suka yi watsi da yarjejeniyar da May ta kulla da kungiyar Tarayyar Turai kan ficewar kasar daga cikinta.
A zaman Majalisar na yau wanda zai fayyace makomar kasar kan ficewarta daga kungiyar akalla ‘yan Majalisu 242 ne suka mara baya ga Firaministar inda suka amince da kunshin yarjejeniyar.
Yanzu haka dai kasa da mako biyu ya ragewa Birtaniya ta fice daga kungiyar ta Tarayyar Turai kamr yadda aka tsara ficewar a ranar 29 ga watan Maris din da muke ciki.
Theresa May dai ta sake nanatawa Majalisar muhimmancin cimma yarjejeniyar kafin ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai, ko da dai Jagoran adawa Jeremy Corbyn ya ce Jam’iyyarsa na da na ta tsare-tsaren ficewar Birtaniyar daga EU.

Exit mobile version