An Mayar Da Yara Fiye Da 400 Makaranta A Jihar Katsina  

 

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina           

Kwamitin kare hakkin yara na wanda kuma yake karkashin shirin “Lifestep” na asusun kula da kananan yara na “Save The Children” ya yi nasarar maido da yara fiye da 400 makarantu a garin Bagiwa da ke karamar hukumar Mani a jihar Katsina.

Babbar manufar shirin shi ne dawo da kananan yara da suka kauracewa  makarantu saboda wani dalili ko na rashin kulawar iyaye da kuma wadanda ba a kai kasa su ba, tare da koya sana’o’i ga iyaye mata domin samun dan abin da zai taimaka wajen dorewar yara zuwa makaranta, wanda kuma a ka shirya babban taro a garin na Bagiwa.

Kazalika shirya taron masu ruwa da tsaki a karamar hukumar na da nufin tattaunawa tare da lalubo hanyoyin da za a kara inganta wannan shiri na kare hakkin yara, tare da bayyana wasu matsaloli da suke damun al’umomim wannan yanki ta yadda za a shawo kansu a nan gaba.

A nasa jawabi a wajen taron,  jami’in na musamman a daga Asusun (Save the Children) na jihar Katsina Yusuf Musa, ya bayyana irin ayyukan da suke yi wanda yake hadin gwiwa tare da kwamitin kare hakkin yara da kuma irin taimakon da suke bayarwa.

Ya kara da cewa suna bada taimakon kayan makaranta da suka hada da kayayyakin wassani da kuma taimako ga iyayen yara saboda a samu dorewar karatunsu.

Da yake nasa bayanin, sakataren kwamitin kare hakkin yara na karamar hukumar Sunusi Lawal Bagiya ya yi bayani game da irin matsalolin da suke fuskanta wanda ya ce sai an dauki mataki na gaggawa idan ana son cimma nasara, saboda yadda yara suke fama da tafiya mai tsawo kafin su je inda za su samu karatun sakandare a wannan yanki.

Har ila yau wannan kwamiti na kare hakkin yara yana wani aiki na musamman a kan karatun manya, inda ya zuwa yanzu fiye da mutane 90 ne suke dauka darasi a garin na Bagiwa kuma sun bayyana gamsuwarsu da yadda ake tafiyar da shirin.

Exit mobile version