Ana zargin maza biyun da suka yi wa wata mata fyade da watsa mata sinadarin acid, bayan da aka bayar da belinsu.
‘Yan sanda sun ce ta zargi mutane biyun ne da wani mutum da ba ta ganeshi ba da watsa mata sinadarin acid ranar Litinin, bayan da ta ki amincewa da yin watsi da shari’ar da ake yi da su.
A watan Mayu ne suka yi mata fyaden a birnin Farrukhabad da ke jihar Uttar Pradesh a Arewacin Indiya. Mutum uku aka tsare a kan laifin, inda har yanzu daya daga cikinsu ya ke tsare.
Tuni ‘Yan sandan suka kaddamar da samame don kamo biyun da ake zargi.