Connect with us

ADON GARI

Mazan Yanzu Suna Son Mace Jajirtacciya A Kan Sana’a – Zainab Ahmad

Published

on

Bakuwarmu ta Adon Garin wannan makon, ta tsage wa ‘yan matan wannan zamanin gaskiya a kan sana’a. Haka nan ta  bayyana musu sirrin da ke cikin sana’a musamman abin da ya shafi kwalliya da ta fi sani kuma ta fi wayau a ciki. A karanta hirar har karshe a ji wadannan da sauran batutuwa, kamar haka:

 

Da farko dai masu karatu za su so su fara da sanin sunanki da dan takaitaccen tarihinki.

Sunana Zainab Hussaini Ahmad, an haife ni a garin Kano, na taso a unguwar Yalwa Goran Dutse, na yi karatu a ‘Yandutse Nazare da Firamare, na bar ‘Yandutse daga JSS1 na koma Sheik Bashir. Na yi islamiyya ta a nan Goran Dutse makarantar Sheik Muhmud Barnoma Sira.

 

Yanzu a bangaren aiki, karatu ko kuma sana’a, a wanne mataki kike ko kuwa zaman gida kike?

Gaskia yanzu dai Sana’a nake yi shi kadai ne matakina a yanzu.

 

Masu karatu za su so jin me ya taba faruwa dake a rayuwa ta farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?

Gaskiya abun da ya taba faruwa da ni na farin ciki irin ranar da na bude studio na make up shi ne babban farin cikin dana taba yi.

 

Wacce shawara za ki bawa mutane game da sha’anin rayuwa ta yau da kullum wanda idan suka yi koyi ko amfani da shi rayuwa za ta inganta?

Gaskiya shawarar da zan bawa mutane ita ce su dage akan sana’ar su ga wanda basa yi su kuma su dage su fara sana’a dan ita ce jigon rayuwa a yanzu. Saboda ita sana’a a yanzu tana da matukar anfani gamu mata saboda idan kana sana’a ba ruwanka da bani-bani, yawan cewa a baka yana sawa a kosa da kai gaskiya musamman ga matan auren idan matar tana sana’a za ki ga ba ta cika cewa ai mata komai za ta yi kokari ta yi da kanta kafin ma ta tambaya tayi da kanta, ga ‘yan mata kuma suma yana da mahimmanci su yi sana’a saboda gudun fadawa wata banzar hanya mara anfani, amma idan suna yin sana’a ba abun da zai sa su yi abunda bai kamata ba, gaskiya dan haka ina janyo hankalin mata da su yi sana’a tana da anfani sosai ga rayuwar mata.

 

Masu karatu za su so jin ko kina da aure ne?

Ba nida aure a yanzu.

 

Malama Zainab za mu so ki yiwa masu karatu dan tsokaci akan alfanu ko muce alherin da ke tattare a cikin wannan sana’ taki?

Gaskiya alherin da ke tattare a cikin wannan sana’a nada matukar yawan gaske dan a cikin ta na samu alheri har motar kaina na samu na mallaka a cikin wannan sana’a da wasu abubuwan da damar gaske.

 

Bayan ke da kike mamallakiyar wannan studio akwai wasu da suke amfana da wannan studio naki?

Gaskiya akwai duk da wajan nawa ne amma nakan janyo wadanda ke bukatar tallafawa na matso da su jikina don suga abunda nake yi suyi ma su samu su koya abunda nake yi.

 

Bayan yin wannan make up da kikeyi, ko kina koya wa wadansu daban masu sha’awar irin sana’ar taki?

Sosai muna ko yarwa dan mu koyar da mutane da dama dan a yanzu haka wasu sun bude nasu wajan suna gudanar da sana’ar su.

 

Yanzu misali a ce wani na sha’awar yin wannan sana’a,ma’ana yana so ya shiga cikin ta a dama da shi shin kofar ki a bude take kina maraba da shi sannan ta yaya zai fara?

Kofa a bude take ina maraba da kowa don koyar wannan sana’a ta make up. Idan mutum yana so ya fara koyar irin wanda zai yi sana’a da shi ko kuma iya wanda zaiwa kansa ne kinsan wasu suna ko ya ba lallai sai na sana’a ba zaka iya koya dan kaiwa kanka kai kadai ba sai kaje an maka ba dan haka zaka zo ka biya ka fara zuwa ka koya.

 

Me za ki ce game da yanayi ko muce hali na rayuwa da mata suka jefa kansu a ciki a yanzu, Musamamman ‘yan Mata?

Gaskiya abin da zance ga ‘yan mata na yanzu ya kamata ‘yan mata su farga su san me rayuwa take ciki a yanzu saboda ‘yan mata na yanzu basu dauki Sana’a da mahimmanci ba sun fi so suyi ta rokar samarinsu wasu suna wulakantasu wasu kuma sai sun neme wata bukata a garesu wadda za ta kaisu ga halaka. Ya kamata ‘yan mata dan Allah ku mai da hankalin ku waje daya ku kama kanku ku kama sana’a dan ita jigon rayuwa a yanzu idan kana sana’a za su amfanenka wacca ba sai an fada maka ba, ayanzu a haka mazan yanzu suna son mace jajirtacciya a kan sana’a saboda sana’a tana debe wa mata kewa da yawan cewa a ba su.

 

Malama Zainab ko akwai wani sako da kike so ki isarwa wasu masu karatu ko wannan jarida wanda bamu tambaya ko ambace shi ba?

Gaskiya sakon da nake so na isar shi ne ‘yan uwana masu harkar make up na area musamman na garin kano ya kamata a dinga hada kai wa ‘yan kasan suna kasa da kai kadinga taimaka musu suma su samu su kai matakin da ya kamata su kai wai dan kaga ana yayin ka kace kai kadai zaka anfani ba shi komai na duniya lokaci kuma mai wuce wane, dan haka ga wa’yanda suke son wannan harka suyi kokari su shigo cikinta kuma ni duk da ina make up gaskiya ba shi kadai ne sana’ar da nake a yanzu ba bacin make up ina harkar girke-girke kala-kala kuma da sauran abunda ba a rasa ba don haka ba lallai sai sana’a make up na idan baka so akwai sana’a da dama wanda zata tallafa ma a rayuwa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: