Daga Khalid Idris Doya
Wasu mazauna yankin Omuo Ekiti, shalkwatar karamar hukumar Ekiti ta gabas, an zargesu da kashe wani mai matsakaicin shekaru bisa zarginsa da kokarin yin garkuwa da wani yaro a yankin.
A daidai lokacin da ‘yan sandan jihar suke tabbatar da faruwar lamarin, sun gargadi jama’a da su daina daukar doka a hannunsu ta hanyoyin da ba su dace ba wajen afkawa ga wadanda suke zargi.
An kuma yi zargin cewa marigayin ya yi kokari da yunkurin yin garkuwa da wani yaro karami dan kimanin shekara bakwai ne wanda kuma ya gaza cimma nasara daga bisani fusatattun matasan yanki suka farmakeshi.
Majiyoyin sun kara da cewa lamarin ya faru ne wajajen karfe 2:00pm a daidai lokacin da yaron ke hanyarsa ta dawowa daga makaranta.
Sannan, mutumin an gano shi na kokarin daukan yaron da karfin tsiya gami da jansa zuwa cikin wani daji da ke kusa, lamarin da ya sanya yaron ihu gami da jawo hankalin jama’an da ke giftawa.
Biyo bayan samun mutsin lamarin, wasu mazauna yankin wadanda mafiya yawansu matasa ne sun garzaya zuwa wurin inda suka cafki wanda suke zargi kana da daka masa wawan dukan tsiya lamarin da ya jefasa ga suma daga baya ya mutu.
“Wanda ake zarfin ya na kokarin sace yaron ne a lokacin da ke hanyarsa ta komawa gida daga makaranta. Ya dauki yaron tare tare da kokarin jansa zuwa cikin daji.
“Bayan da jama’a suka hango shi sun shelanta wa sauran jama’a ga abun da ke faruwa inda nan kuwa suka cakameshi da duka.”
Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta tabbatar da faruwar lamarin, ta nanata cewar marigayin bayan da ya sha bugu ne har hakan ya kai ga mutuwarsa, bugun wanda jama’an yankin suka masa.
Abutu ya ce daya daga cikin shugabannin unguwar Iludufin shine ya kai rahoton faruwar lamarin ga caji ofis inda suka tura jami’ansu na ‘yan sanda nan take.
PPRO na cewa, “Cikin gaggawa jami’anmu suka hanzarta zuwa wajen da kokarin ceto mutumin, sun wuce da shi caji ofis domin neman kariya da kokarin kaishi asibiti cikin hanzari domin neman kulawar likita,”
“Abun kaici, ya mutu a caji ofis sakamakon dukan tsiya da ya sha daga wajen matasan,” in ji PPRO.
Ya shaida cewar gawar mamacin an kaita zuwa dakin adana gawarwaki dake babban asibitin Omui Ekiti, yayin da kuma suka kaddamar da bincike kan lamarin domin kara samo bayanai.
Daga bisani kuma sai ya jawo hankalin jama’a da cewa suke daina daukar doka a hannunsu domin yin hakan ka iya zama rashin adalci, a cewarsa wadanda ake zargi ba za su taba zama masu laifi ba har sai an tabbatar da hakan.
Ya bada shawarar cewa duk wani da ake zargi a tsareshi ko a kamashi gare da mikasa ga jami’an ‘yan sanda domin su gudanar da nasu binciken tare da gurfanar da shi a kotu har zuwa lokacin da hukunci za ta tabbatar ya aikata laifin da ake zarginsa ko a’a.