Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Mazauna Gundumar Yanling Na Kokarin Tabbatar Da Zaman Al’umma Mai Matsakaicin Karfi

Published

on

Ana kiran gundumar Yanling ta birnin Xuchang na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin, da garin furanni da tsirrai. A cikin ’yan shekarun nan, gundumar ta hada halinta na musamman da manufar ci gaba irin ta kiyaye muhalli ta “dutsen dake da bishiyoyi dutse ne dake cike da arziki”, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, da nufin inganta sana’ar shuka furanni da tsirrai zuwa hanyar ci gaba mai inganci. Ba ciyar da sana’ar ta gargajiya gaba kadai aka yi ba, har ma da kara kyautata zaman rayuwar mazauna wurin.

Tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce, sannu a hankali gundumar Yanling ta kasance wani muhimmin wuri na shuka da sayar da furanni da tsirrai a nan kasar Sin, ta yadda kuma mazauna wurin suka kawar da talauci.
A shekarar 2013, Wu Xiaoying da mijinta suka karbi lambun renon tsirrai daga hannun mahaifinta. Amma, bukatun kasuwa ya sauya, ba bukatar tsirrai don kiyaye muhalli kadai ake ba, har ma domin kawata muhalli. Hakan ya sa Wu Xiaoying ta gamu da matsala wajen ci gaba da sana’ar. Yaya za a yi a nan gaba?
Gundumar Yanling ta soma kokarin inganta shuke-shuke ta hanyar kimiyya, ta kuma tsara ma’aunin kaya guda 12 da ka’idojin shuke-shuke guda 16. Kana ta hada kai da jami’o’i da kwalejoji da hukumomin nazarin kimiyya sama da 30, don taimakawa masu shuka furanni da tsirrai wajen shigo da nau’o’i masu inganci.
A cikin ’yan shekaru, sai fadin shuke-shuke na iyalin Wu Xiaoying ya karu daga muraba’in mita kusan dubu 15 zuwa zuwa dubu 60 da wani abu. Ta ce, sun gamu da wata damar ci gaba mai kyau. (Mai fassarawa Bilkisu Xin)
Advertisement

labarai