Mazauna Kuje Sun Bayyana Bukatursu Ga Sabon Shugaban Karamar Hukumar

Wasu daga cikin mazauna karamar hukumar Kuje da ke karkashin babban birnin tarayya Abuja, sun yi kira da sabon shugaban karamar hukumar Kuje, Mista Abdullahi Sabo, cewar ya maida hankalin shi a kan matsalolin da su ke damuwar al’ummar yankin, wadanda su ka hada da  abubuwan more rayuwa, bangaren ilimi, da kuma muhalli, domin cigaban karamar hukumar. Sun yi wannan kiran ne a wata ganawa da su ka yi da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar Litinin.

Mista Abraham Gado, mazaunin garin Kuchiya da ke cikin karamar hukumar Kuje ya bayyana cewar, ba wani cigaban da a ka samu a karamar hukumar. Ya kara bayanin cewar, ita karamar hukumar ta rasa wasu muhimman abubuwan musamman na more rayuwa wadanda su ka lalace saboda rashin kulawa.

Gado ya yi kira ga shi sabon Shugaban karamar Hukumar da cewar, ya kamata ya dauki kwararan matakai, musamman wajen kammala ayyukan da a ka fara , amma an kasa kammala su, kamar hanyoyin mota, yin sababbin hanyoyi ta bayan gari wadda za ta taimaka wajen rage cunkoson abubuwan hawa musamman ma lokacin da kowa  ke son komawa gida lokacin da aka tashi aiki. Ya cigaba da bayanin cewar,  “ba wani aikin a zo a gani da tsowan shugaban karamar hukuma ya yi musamman ma wajen abubuwan more rayuwa. Ga kuma ayyuka masu yawa wadanda bai kammala su ba.

“Da akwai bukata bunkasa karamar hukumar Kuje. ’Yan Nijeriya kullun kwakwalwarsu kara wayewa, ta ke yi, idan da a ce yayi aiki tukuru, wannan shi za a iya amfani da shi wajen sa ke zaben shi, nan da shekaru uku masu zuwa.

Esther Kure wadda ta ke unguwar Shadadi, ta yi kira gare shi ya gyara hanyoyin da su ka lalakce, ga kuma rashin ruwa a ita karamar hukumar, sai kuma rashin wutar lantarki. Kure wadda ta kara cewar, su mutanen karamar hukumar an ma manta da su ne gaba daya, ba su wani jin dadin mulkin farar hula ba, don haka ta yi kira ga shi sabon shugaban karamar hukumar da ya ceto mutanen karamar hukumar.

Obina Eze wanda shi kuma dan kasuwa ne, shi ma ya yi kira ne ga shi sabon Shugaban karamar hukumar cewar, ya rage kudin da a ke biya wajen yin hayar shago a kasuwar Kuje,saboda yin hakan zai kara bunkasa harkokin kasuwanci. Eze ya kara bayyana cewar, ba wata kasar da za ta cigaba  idan dai  ba a hada  al’amuran tattalin arziki ta hanyar hada – hadar kasuwanci. “Gwamnatoci a shekarun baya, ba su bayar da muhimmanci a kan wadanda su ka cimma burin cigaba, ba su wuce wadanda su ba ruwan su da girman kai. “Sabo ya kamata ya rage kudaden da a ke bayarwa na a shiga kanti ko shago a cikin kasuwa, saboda kasuwanci ya bunkasa.

Exit mobile version