Connect with us

LABARAI

Mazauna Libiya Da Suka Dawo Nijeriya Sun Samu Aiki

Published

on

‘Yan ci-ranin kasar Libiya da gwamnatin tarayya ta  dawo da su kasarsu ta haihuwa sun samu aikin yi daga kungiyoyin da ke kula wa da rayuwar marasa galihu.

Bayan dawo wa da su kasarsu ta haihuwa an koyar da su sana’o’i daban-daban, musamman harkar  kasuwanci da kuma abin da ya shafi harkar noma ta zamani.

kimanin  mutum 1,130 ne suka amfana da wanan shirin na bunkasa harkokin dogaro da kai daga jihohi da dama. Kamar jihar Nasarawa da Edo da Kano da Kaduna da ma jihar Legas.

‘Yan ci-ranin da aka dawo da su kasarsu ta haihuwa a ranakun 27 da 31 ga watan Agusta an koyar da su harkokin Sana’a ta zamani a Birnin Ikko da ke tarayya Nijeriya.

Sashin kungiyoyin da suka koyar da wadannan bayin  Allah sun hada da kungiyar IOM da ta UN ta koyar da su sana’o’in hannu kala-kala. Aka kuma taimaka musu da tallafi na masamman.

An kuma bukaci wadanda suka samu wanan shirin ta harkokin Sana’a da su maida hankali a kan abubuwan da suka koya saboda zai rike kowa tare da tallafa wa iyalansa maza da matane aka koyar da su aka kuma taimaka musu a wannan hanyar.

UN da IOM sun hada karfi da karfe da gwamnatin tarayya ta hanyar bunkasa jindadin rayuwar al’umman da suka samu kansu a rin wannan rayuwar masamman ta janibin gudun hijira ko makamancin haka.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: