Connect with us

RIGAR 'YANCI

Mazauna Saudiyya Ne Kawai Za Su Yi Aikin Hajjin Bana

Published

on

Ta tabbata cewa dai al’ummar musulmi daga sassan kasashen duniyar nan ba za su samu zuwa aikin Hajjin bana ba, domin sai mazaunin kasar Saudi Arebiya ne kadai zai samu wannan damar, kamar yadda Hukumar kasar ta Saudiyya ta sanar a kwanakin baya.

Wata jaridar kasar ta Saudiyya ‘The Arab News’ ta ruwaito ma’aikatar Kula da aikin hajji da Umra ta kasar tana cewa, aikin Hajjin bana wanda za a fara shi a wata mai zuwa, jama’a kalilan ne za a ba dama su yi, wanda ta ce daukar wannan mataki ya zama dole bisa la’akari da irin barazanar da cutar Korona ke yi ga lafiyar al’umma a duk fadin duniyar nan.
Ma’aikatar kula da aikin Hajjin da ta Saudiyyar ta ci gaba da bayyana cewa, al’ummar kasashe daban-daban ne za su samu sauke faralin, amma dole sai wadanda su ke kasar ta Saudi Arebiya.
Ma’aikatar kula da aikin Hajjin ta ce, “mutane kalilan ne za a bari su gudanar da aikin Hajjin bana daga kasashe daban-daban, amma wadanda ke zaune a Saudi Arebiya a halin yanzu. An dauki wannan mataki ne don ganin an gudanar da aikin Hajji mai tsafta, musamman game da cututtuka, tare da daukar duk matakan da suka wajaba wajen rage cunkoson jama’a, ta hanyar bayar da tazara tsakanin juna.
Bisa wannan sanarwa ta kasar Saudiyya, Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta kasar nan, NAHCO ta sanar da cewa yanzu zabi biyu ne ya rage ma wadanda suka riga suka biya kudadensu don sauke faralin, ko dai su ajiye sai badi in Alah ya kai mu, ko kuma a dawo masu da kudadensu.
Shugaban Hukumar kula da jin dadin Alhazan, Zikrullah Kunle Hassan ne ya bayyana haka Abuja, inda ya ce “sakon mu ga maniyyata Hajjin bana shi ne, imma dai su karbi kudadensu, ko kuma su ajiye a wurinmu sai aikin Hajji na badi.”
Advertisement

labarai