Mazauna Xinjiang Sun Musanta Zargin Aikin Tilas A Jihar

Mazauna Xinjiang

Daga CRI Hausa,

Wakilan yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kai dake shiyyar arewa maso yammacin kasar Sin, sun karyata karairayi masu alaka da ‘yan adawar kasar Sin dake kasar Amurka da yammacin duniya.

Amatjan Abduhalik, mataimakin shehun malami a sashen nazarin harkar kudi da tattalin arziki na jami’ar Xinjiang, ya bayyana a taron manema labarai cewa, manufofin dake shafar ayyukan kwadago da sana’o’in dogaro da kai sun dace da dokokin kasar Sin da kuma dokokin hukumar kwadago ta kasa da kasa da dokokin hakkin bil adama.

Amatjan Abduhalik, ya kara da cewa, “Batun da ake kira da suna ‘aikin tilas’ a jihar Xinjiang, karya ce da ake yadawa a wannan zamani.”

Abdusalam Hoji, wanda ke aiki da kamfanin silicon a yankin, ya ce kamfanin ba shi da wani abu mai kama da “aikin tilas.”

A cewarsa, ya fara aiki da kamfanin ne a watan Satumban shekarar 2020, kuma kamfanin yana da gidajen sayar da abincin halal na kananan kabilu kuma ya tanadi gidajen zama ga ma’aikatansa kyauta.

Amar Jelil, wani manomin auduga dake birnin Korla, ya ce yana daukar hayar karin ma’aikata domin girbin auduga a lokacin kaka kuma yana biyan su hakkokinsu bisa yarjejeniyar da suka cimma tare da su.

Ya kara da cewa, a yanzu, kowa yana amfani da manyan motocin aikin gona ne in banda tsirarun ma’aikata masu aikin hannu da ake bukata.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

Exit mobile version