Connect with us

WASANNI

Mbappe Ba Zai Buga Kofin Zakarun Turai Ba

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain, Kylian Mbappe, wanda ke fama da rauni a kafarsa ba zai samu fafatawa a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar zakarun nahiyar Turai tsakanin kungiyarsa da Atalanta a birnin Lisbon ranar 12 Agusta ba.

Mbappe, mai shekaru 21 a duniya, ya samu rauni a idon sawunsa ne a ya yin wasan karshe na kofin kalubalen Farasansa da PSG ta kara da Saint-Etienne a ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin da ya sa zai shafe makonni 3 ba tare da ya buga wasa ba.
Sai dai yana iya dawowa a wasan  kusa da na karshe idan har kungiyar ta sa ta samu nasarar tsallakewa amma kuma duk da haka ba karamin kalubale kungiyar zata fuskanta ba na rashin dan wasan gaban wanda shine yake zurawa kungiyar kwallo a raga.
dan wasan na kasar Faransa ya fita daga filin wasa yana hawaye bayan da dan wasan baya na Saint-Etienne Loic Perrin ya rafke shi kafin a tafi hutun rabin lokaci kuma daga baya likitoci suka bayyana cewa ciwonsa ,mai tsanani ne.
Publicité
Sakamakon tsaikon da annobar coronabirus ta janyo a kowane fanni na rayuwa har ma da wasannin kwallon kafa, karkare gasar zakarun nahiyar Turai ta bana zai hada ne da fafatawa irin ta sili daya kwale tsakanin tawagogi 8 da za a yi a Lisbon babban birnin Portugal, ana kuma sa ran buga wasan karshe a ranar 23 ga watan Agusta.
Kociyan kungiyar kwallon kafar ta PSG, Thomas Tuchel, ya bayyana cewa sun samu babbar matsala rashin dan wasan gaban na kasar Faransa sai dai yace duk da haka za suyi iya yinsu domin ganin sun ci gaba da samun nasara duk da babu dan wasan.
Advertisement

labarai