Daga Abba Ibrahim Wada
Tsohon wakilin ɗan wasan Barcelona, Josep Maria Minguella, ya bayyana cewa ɗan wasan gaba na ƙasar Faransa, Kylian Mbappe ya fi son komawa Barcelona ba Real Madrid ba ko PSG.
Minguella ya ce, shugaban gudanarwar ƙungiyar ta Barcelona Josep Maria Bartemeu shi ne mai laifi domin bai mayar da hankali akan Mbappe ba.
Ya ci gaba da cewa, “tun lokacin da Mbappe ya ji labarin Neymar zai bar Barcelona ya yanke shawarar komawa ƙungiyar domin ya san zai samu abinda yake so, zai samu lokacin buga wasa, sannan zai samu ɗimbin magoya baya.
Ya ƙara da cewa, “ɗan wasa Mbappe za iyi araha, ba zai yi tsada ba idan Barcelona taso ɗaukarsa, domin yana son ƙungiyar, kuma sun iya cinikin ɗan wasa ba kamar PSG ba.”
A ƙarshe Minguella ya ce, “akwai lokutan da ya fahimci ra’ayin Mbappe, ya san ba ya son Madrid ko PSG, kawai yana son buga wasa tare da Messi ne kuma yana son kasancewa a Barcelona.
Minguella dai shi ne ya taimakawa Barcelona ta siyo Maradona daga Napoli da Riɓaldo ɗan ƙasar Brazil.