Khalid Idris Doya" />

MDD Ta Koka Kan Karancin Kudin Taimaka Wa Wadanda Guguwar Idai Ta Shafa

Majalisar dinkin duniya MDD ta ce ba a amsa sosai ba, game da kiran da ta yi na neman kudin gudanar da ayyukan agaji ga miliyoyin mutanen da mahaukaciyar guguwar Idai ta sha a yankin Kudancin Afrika.
Stephane Dujarric, Kakakin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, a kasar Mozambikue da guguwar ta fi shafa, kaso 21 na dala biliyan 282 da ake nema kadai aka samu.
Ya bayyana haka ne bisa dogaro da bayanan da ofishin kula da harkokin agajin jin kai na majalisar da abokan hulda a fanni ayyukan agaji da kuma kasashen da guguwar ta aukawa, suka bayar.
Adadin wadanda suka mutu da gwamnatin kasar Mozambikue ta bayar a baya bayan nan, ya kai 598, inda ake tsammanin karuwarsa saboda samun hanyar shiga sauran yankuna da iftila’in ya shafa.
A Zimbabwe kuwa, abokan hulda na ayyukan agaji da gwamnatin kasar, sun kaddamar da asusun neman tallafi ga kasar, inda suke neman dala biliyan 60 domin agazawa mutane 270,000 da mahaukaiyar guguwar ta shafa.
Gwamnatin Zimbabwe ta tabbatar da mutuwar mutane 299 yayin da wasu 300 suka bata.
Ayyukan agaji a Malawi kuwa na bukatar dala miliyan 26, domin cika dala miliyan 45.2 da ake bukata na gudanar da ayyukan agaji.

Exit mobile version