Bello Hamza" />

MDD: ‘Yanci Dan Adam Na Fuskantar Barazana A Duniya

An bude taro shekara-shekara na MDD a kan sha’anin kare hakkin bil Adama karo na 40 a Geneba, wanda a taron babban sakataran MDD António Guterre ya ce duniya na fuskantar barazana.
A lokacin da yake jawabi a wajen taron sakataran MDD António Guterre ya yi kiran da a kawo karshen wariyar jinsi da rashin juriya kuma ya ce da sannu a hankali ‘yancin dan Adam na samun koma baya a kasashen duniya da dama. Kana ya yi Allah wadai da karuwar ‘yan mulkin populiste abin da ya ce hadari ne da kuma ci gaba da yada jawaban kiyaya a kafofin sada zumunta.

Exit mobile version